Yanzu Yanzu: Dan majalisan Cross River ya fadi ya mutu

Yanzu Yanzu: Dan majalisan Cross River ya fadi ya mutu

Dan majalisa dake wakiltan mazabar Obudu a majalisar jihar Cross River, Mista Steven Ukpukpen, ya fadi ya mutu a yayin motsa jiki da safiyar ranar Laraba.

Lamarin ya afku ne da misalin karfe 7:00 na safe a hanyar Moore dake Calabar.

An rahoto cewa anyi gaggawan kai dan majalisan wani asibitin sojin ruwa dake kusa, amma likitan dake kan aiki yace yana cikin mawuyacin hali don haka ya tura su wani asibiti.

Likitocin wani asibitin kudi da aka kai shi ne suka tabbatar da mutuwarsa. Sannan kuma asibitin koyarwa na jami’ar alabar ma da aka kai shi daga baya sun tabbatar da cewa ya mutu.

Yanzu Yanzu: Dan majalisan Cross River ya fadi ya mutu

Yanzu Yanzu: Dan majalisan Cross River ya fadi ya mutu

Da yakemartani kan lamarin, kakakin majalisar, Mista Gaul-Lebo yace yana cikin alhini kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dan majalisar wakilai daga Arewa ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

A halin da ake ciki, Sanata Dino Melaye ya bayyana sauya shekarsa daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za a karrama gwamnoni 5 da suka fi yiwa jama’a aiki, duba bangaren da kowanne yafi dagewa

Gwamnonin Najeriya 5 da suka fi yiwa jama’ar su aiki da bangaren da kowanne yafi dagewa, za a karrama su

Za a karrama gwamnoni 5 da suka fi yiwa jama’a aiki, duba bangaren da kowanne yafi dagewa
NAIJ.com
Mailfire view pixel