Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye ya koma PDP

Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye ya koma PDP

Labarin da ke shigo mana yanzun nan na nuna cewa sanata mai wakiltan Kogi ta yamma ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP da safen nan. Sanatan ya bayyana sauya shekarsa ne a zauren majalisa a yau.

Takaddama tsakanin Sanata Dino Melaye da gwamnatin tarayya ya fara ne tun lokacin da hukumar yan sandan Najeriya ta alanta neman Dino Melaye ruwa a jallo bisa ga zargin daukan nauyin wasu yan baranda a jihar Kogi.

Hukumar shiga da ficen Najeriya ta damke Sanata Dino Melaye a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayinda yake kokarin zuwa kasar Maroko.

Daga baya hukumar yan sanda suka garkameshi domin gurfanar da shi a kotu a garin Lokoja, jihar Kogi, amma sanatan ya tsallo daga cikin motan sanda kuma ya ji rauni.

KU KARANTA: Kannywood: Ba zan taba shiga harkar siyasa ba – Ali Nuhu

Haka dai aka cigaba da kai komo tsakanin hukumar yansanda da Sanatan daga asibiti zuwa kotu. daga karshe dai kotu ta bada belinsa.

Masu sharhi sun bayyana cewa an yi masa sanatan bita da kulli ne bisa ga maganganun batancin da yake yiwa shugabancin shugaba Buhari da kuma jam'iyyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
2019: Atiku ya yi alfahari da kwarewar sa a warware wata matasalar da ya ce tafi damun Najeriya

2019: Atiku ya yi tutiya da kwarewarsa a wata matsala da take addabar Najeriya

2019: Atiku ya yi alfahari da kwarewar sa a warware wata matasalar da ya ce tafi damun Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel