Sultan ya yi kaca-kaca da wani gwamna da tsohon minista a kan alakanta kisan makiyaya da Danfodio

Sultan ya yi kaca-kaca da wani gwamna da tsohon minista a kan alakanta kisan makiyaya da Danfodio

- Kungiyar Jama'atu Nasril Islam karkashin jagorancin Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar III ta nuna rashin jin dadin ta a kan wasu furuci da Gwamna Ortom da Femi Fani-Kayode su kayi

- Kungiyar musulmin ta karyata ikirarin da gwamnan da tsohon ministan su kayi na danganta makiyaya masu kisa da jihadin marigayi Usman Danfodio

- Kungiyar ta shawarci al'ummar musulmi su dage da addu'o'i a yanzu da muke tunkarar zaben 2019

Kungiyar Jama'atul Nasril Islam karkashin jagorancin Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar III tayi kaca-kaca da gwamna Samuwl Ortom na jihar Benue da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode saboda cewa kashe-kashen makiyaya a jihohin Benue, Taraba da wasu sassan arewa cigaban jihadin marigayi Usman Danfodio ne.

Sarkin musulmi ya yi kaca-kaca da gwamna Ortom da Fani-Kayode a kan wasu kalamai da suka furta
Sarkin musulmi ya yi kaca-kaca da gwamna Ortom da Fani-Kayode a kan wasu kalamai da suka furta

Sultan Sa'ad Abubakar III, wanda shine shugaban kungiyar ya gargadi gwamnan da ma wasu masu ra'ayi irin nasa da su dena takala musulmin Najeriya a lokacin da ya yi magana a hedkwatan kungiyar da ke jihar Kaduna.

KU KARANTA: Fitattun jaruman Indiya 6 da suka taba ziyartar dakin Allah

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, kungiyar Jama'atun ta kuma shawarci al'ummar musulmi su dage da addu'o'i na zaman lafiya musamman yanzu da ake tunkarar zaben kasa na 2019 duba da yadda wasu yan siyasa ke kokarin tayar da fitina a kasar.

Kamar yadda sanarwan ta fito ta bakin sakataren kungiyar, Abubakar Khalid Aliyu, Kungiyar bukaci musulmi su kara dage wajen yiwa kasan nan addu'an samun zaman lafiya da kuma yin zaben 2019 cikin zaman lafiya duk da irin kalamen da yan siyasa ke yi.

Wannan dai mayar da martani ne a kan wasu kalamai da gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya furta yayin wata hira da akayi dashi a wani shiri mai suna The Osasu Show a wata gidan talabajin da ke Makurdi inda ya ce kashe-kashen da makiyaya ke yi cigaban jihadin Usman Danfodio ne.

A baya, shima tsohon ministan sufurin jiragen sama a zamanin mulkin Obasanjo, Femi Fan-Kayode a ya fadin abubuwa masu kamaceceniya da wannan na danganta kashe-kashen makiyayan da jihadin Usmanu Danfodio.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel