Barayin Shanu sun salwnatar da rayuka 3 da raunata mutane 4 a jihar Kaduna

Barayin Shanu sun salwnatar da rayuka 3 da raunata mutane 4 a jihar Kaduna

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne mutane uku suka riga mu gidan gaskiya tare da jikkatar wasu mutane 4 a kauyen Kurega dake karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Hukumar 'yan sandan jihar ta tabbatar da wannan ibtila'i da ya afku a yankin karamar hukumar Chikun dake kan iyaka da karamar hukumar Birnin Gwari, inda ta ce babu wanda ake zargi da wannan ta'addanci face barayin shanu.

Kakakin hukumar na jihar, ASP Mukhtar Aliyu ya bayyana cewa lamarin ya afku da misalin karfe 2.00 na tsakar ranar Talatar da ta gabata yayin ganawa da manema labarai.

Barayin Shanu sun salwnatar da rayuka 3 da raunata mutane 4 a jihar Kaduna
Barayin Shanu sun salwnatar da rayuka 3 da raunata mutane 4 a jihar Kaduna

A yayin da yake fashin baki ga 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Najeriya, babban jami'in ya bayyana cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu shanu bayan sun tafka ta'asa, sai dai ya bayar tabbacin cewa hukumar ta bazama domin bin sahun wannan miyagu.

KARANTA KUMA: Ba bu lallai Mafi 'Karancin Albashi ya samu shiga zuwa watan Satumba - Ngige

Legit.ng ta fahimci cewa, kawowa yanzu ba bu wani da ya shiga hannun jami'an da ake zargi da wannan aika-aika, inda binciken 'yan sanda ya tabbatar da cewa mutane sun jikkata yayin da rayuka uku ne kacal suka salwanta sabanin jita-jitar salwantar rayuka takwas.

ASP Aliyu ya nemi mazauna wannan yanki akan bayar da hadin kai ga jami'an yayin gudanar da bincike domin ganin wannan miyagu sun shiga hannu wajen sauke nauyin su na kare al'umma da kuma dukiyar su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel