Idan ma ka so kana iya canja mana suna – Majalisa ta maida martani ga Jega

Idan ma ka so kana iya canja mana suna – Majalisa ta maida martani ga Jega

- Majalisar wakilai ta nuna rashin jin dadinta ga zargin da tsohon ciyaman na hukumar zabe mai zaman kanta, Attahiru Jega, yayi masu da rashawa

- Majalisar dattijai tayi ikirarin cewa Jega yana da damar fadin ra’ayinsa, saboda haka zai iya fadar abunda ransa ya bashi

- Mambobin majalisar wakilai sun kalubalanci Jega akan ikirarinsa da cewa ya lissafo jerin sunaye mambobin masu aikata rashawa

Majalisar wakilai a ranar Litinin, 28 ga watan Mayu, ta mayar da martani akan zargin da tsohon ciyaman na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Attahiru Jega, yayiwa ‘yan majalisar.

Mai magana da yawun majalisar Aliyu Sabi Abdullahi, lokacin da yake mayar masa da martani yace Jega na da damar fadar duk abunda yaga dama.

‘Yan majalisar sun bukaci ya bayyana jerin sunayen wadanda ke aikata rashawa.

Idan ma ka so kana iya canja mana suna – Majalisa ta maida martani ga Jega
Idan ma ka so kana iya canja mana suna – Majalisa ta maida martani ga Jega

Abdullahi yace “Jega na iya canza masu sunaye ma idan yaga dama zuwa duk sunan da yayi masa. Jega nada iko akan ra’ayinsa, wanda kuma hakan bazai canza abunda yake na zahiri ba.

“wannan shine dadin dimokuradiyya. Mutane suna da damar fadin abunda sukaga dama. Wannan damarsu ce. Saboda haka bazance komai ba akan abunda ya fada."

KU KARANTA KUMA: Ranar Jimami: ‘Yan Najeriya sun roki shugaba Buhari da ya magance kisan da akeyi a fadin kasar

Idan dai zaku tuna a ranar Litinin, 28 ga watan Mayu tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta arfesa Attahiru Jrga ya bayyana cewa babu wanda ya kai yan majalisa rashawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel