Shugaba Buhari ya lissafo canjin da aka samu cikin shekaru 3 a Gwamnatin sa

Shugaba Buhari ya lissafo canjin da aka samu cikin shekaru 3 a Gwamnatin sa

- Yau Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta cika shekaru da kafuwa

- Shugaban Kasar ya dai bayyana irin nasororin da aka samu a Gwamnatin

- Daga ciki akwai bunkasa harkar noma da kuma maganin barayin Najeriya

A yau dinnan ne Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari ta cika shekaru 3 da kafuwa. Yanzu haka ana ta bukukuwan Ranar Damukaradiyya a Kasar. Haka kuma Najeriya dai tayi shekaru 19 cur a jere ana karkashin mulkin farar hula.

Shugaba Buhari ya lissafo canjin da aka samu cikin shekaru 3 a Gwamnatin sa
Shugaba Buhari ya cika shekara 3 a kan karagar mulkin Najeriya

Gwamnatin Shugaba Buhari tana cigaba da zayyano irin manyan ayyukan da tayi cikin shekaru 3 a kan karagar mulkin kasar. A jiya dai Fadar Shugaban Kasar ta lissafo wasu ayyuka 9 da Gwamnati tayi domin cigaban Najeriya.

KU KARANTA: Sanatan APC zai yi takara da Gwamna El-Rufai a Kaduna

Ga dai jerin ayyukan da Shugaba Buhari yace Gwamnatin sa tayi nan daga 2015 zuwa yau:

1. Dawo da tattalin arzikin Kasa cikin hayyacin sa

2. Bunkasa harkar noma ta samar da abincin da za a ci

3. Tattalin kudin shigar da Najeriya ta samu daga mai

4. Saukaka harkar kasuwanci a cikin Kasar

5. Maida hankali kan cigaban al’umma

6. Toshe kafar satar dukiyar Gwamnatin Kasar

7. Inganta harkar tsaro da rayukan Jama’a a fadin Najeriya

8. Yi wa bangaren shari’a garambawul da kuma

9. Gyara rayuwar mutanen Yankin Neja-Delta

Sai dai Jam’iyyar adawa ta Kasar watau PDP tace babu wani abin murna a wannan rana domin kuwa kashe Kasar kurum Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi ta kowane bangare cikin shekaru da yayi yana kan karagar mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel