Badakalar samar da wuta: Obasanjo ya fitar da sakamakon binciken da EFCC tayi masa

Badakalar samar da wuta: Obasanjo ya fitar da sakamakon binciken da EFCC tayi masa

Yayin da batun takaddamar nan game da yadda tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya kashe makudan kudade wajen inganta harkar wutar lantarkin kasar ke cigaba da wanzuwa, a jiya ya fitar da wani rahoton bincike da hukumar EFCC ta yi masa a lokacin mulkin marigayi shugaba Yar'adua.

Rahoton da ya fitar mai kunshe da shafuka akalla 20, yana kunshe ne da bayani tiryan-tiryan akan yadda gwamnatin ta sa ta fitar da makudan kudaden da suka kai darajar Dalar Amurka biliyan 16 da sunan aikin habaka wutar lantarkin.

Badakalar samar da wuta: Obasanjo ya fitar da sakamakon binciken da EFCC tayi masa

Badakalar samar da wuta: Obasanjo ya fitar da sakamakon binciken da EFCC tayi masa

KU KARANTA: Kun ga tsohuwa mai shekaru 70 dauke da ciki wata 6

NAIJ.com ta samu cewa hukumar ta EFCC a wancan lokacin karkashin jagorancin shugaban ta Ibrahim Lamorde ta soma binciken tsohon shugaban kasar ne bayan da ta samu takardar korafi da tsohon gwamnan jihar Abia Orji Uzor Kalu.

Sai dai kuma kamar yadda binciken ya nuna, hukumar ta EFCC ta wanke tsohon shugaban kasar daga dukkan zargi inda tace ba ta samu wata kwakkwarar shaida ba da zata tabbatar da kasancewar sa mai laifi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hari la yau: ‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi

Masu garkuwa sun sace matar wani malamin addini a Kaduna bayan sun kashe shi

Hari la yau: ‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi
NAIJ.com
Mailfire view pixel