Kwamacala: An gano ma'aikatan lafiya na boge 6,000 a wannan jihar ta Arewa

Kwamacala: An gano ma'aikatan lafiya na boge 6,000 a wannan jihar ta Arewa

Biyo bayan wani aikin tantancewa da gwamnatin jihar Sokoto dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya ta gudanar akan ma'aikatan lafiyar ta sama da dubu 13 gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal yace akalla dubu 6 an gano duk na boge ne.

Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a yayin da yake kaddamar da wata cibiyar lafiya a matakin farko da kuma dakin ansar haihuwa a unguwar Gagi, dake a cikin birnin Sokoto.

Kwamacala: An gano ma'aikatan lafiya na boge 6,000 a wannan jihar ta Arewa

Kwamacala: An gano ma'aikatan lafiya na boge 6,000 a wannan jihar ta Arewa

KU KARANTA: Musulmai a Najeriya sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Isra'ila

NAIJ.com ta samu cewa Gwamna Tambuwal din har ila yau ya kuma kara da cewa gwamnatin sa na nan na shirin daukar ma'aikatan lafiya akalla dari 4 domin kara inganta harkar lafiya a jihar.

A wani labarin kuma, Sabanin ra'ayoyin mafiya yawan 'yan siyasa a jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, daya daga cikin jiga-jiganta kuma gwamnan jihar Ebonyi, Mista David Umahi ya sha alwashin cigaba da girmama shugaban kasa Muhammadu Buhari duk kuwa da kasancewar su a jam'iyyu daban daban.

Gwamnan dai ya bayyana cewa shi fa shugaban kasar uban gidan sa ne kuma yana mutun ta shi tare da yin fashin bakin cewa ba dole bane sai ya ci zarafin shi sannan ne zai zama dan jam'iyyar PDP na hakika.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Rundunar sojin saman Najeriya ta samu nasarar kashe wasu gungun 'yan ta'adda a jihar Zamfara

Rundunar Sojin saman Najeriya ta samu nasarar kashe wasu gungun 'yan ta'adda a jihar Zamfara

Rundunar sojin saman Najeriya ta samu nasarar kashe wasu gungun 'yan ta'adda a jihar Zamfara
NAIJ.com
Mailfire view pixel