Rikicin Masarautar Saudiyya: Yarima Fahad yayi kira akan yiwa Sarki Salman juyin mulki

Rikicin Masarautar Saudiyya: Yarima Fahad yayi kira akan yiwa Sarki Salman juyin mulki

Wani sabon rahoto da sanadin shafin jaridar TRT Hausa ya bayyana cewa, yariman kasar Saudiyya, Khalid Bin Farhan, ya na neman hadin kai wajen kwace mulkin kasar daga hannun Sarkin Salman.

Yariman yayi ikirarin cewa, a halin yanzu kaso 99 cikin 100 na ahalin masarautar sun shirya tsaf domin karbe karagar mulki daga hannun Sarki Salman da iyalan sa.

Jaridar ta ruwaito cewa, Yariman wanda ya fake a kasar Jamus tun a shekarar 2013, ya nemi wasu 'yan uwan sa masu jinin sarauta akan su hada kai domin yiwa Sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud.

NAIJ.com ta fahimci cewa, Yarima Farhan wanda a halin yanzu yake kasar Jamus a matsayin dan gudun hijira ya yi kira ga Yarima Ahmad bin Abdulaziz da kuma dan uwan sa Yarima Muqrin Bin Abdulaziz akan su zamto tsintsiya madauri daya wajen hadawa Sarki Salman kayan sa a hannu.

Rikicin Masarautar Saudiyya: Yarima Fahad yayi kira akan yiwa Sarki Salman juyin mulki

Rikicin Masarautar Saudiyya: Yarima Fahad yayi kira akan yiwa Sarki Salman juyin mulki

A yayin ganawa da manema labarai na jaridar Middle East Khalid, ya bayyana cewa mulki Sarki Salman ba bu abinda ya haifar face babbar asara ga masarautar ta Saudiyya da kuma duniyar Musulunci baki daya.

KARANTA KUMA: Majalisar Dattawa ta mika Kasafin Kudin 2018 zuwa Fadar Shugaban Kasa

A kalaman sa, "Idan Ahmad da Muqrin suka zama tsintsinya madauri daya, ina da tabbacin cewa kaso 99 cikina 100 na ahalin masarautar Saudiyya, jami'an tsaro da dakarun soji zasu goya musu baya domin sun yi mani alkawarin hakan"

"Ina son na yi amfani da wannan dama domin kiran Kawunnai na Ahmad da Muqrin, 'ya'yan Marigayi Sarki Abdullah bin Abdul-Aziz wanda har ya kwanta dama yana yiwa Addinin Islam hidima, domin dawo da wannan martaba."

Ya kara da cewa, "Kasar Saudiyya dutse ce mai cike makil da wuta wanda ke gaf da yin kwaranya."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Babban sufetan Yansanda ya canza ma rundunar Yansandan SARS suna, karanta

Sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel