Majalisar Dattawa ta mika Kasafin Kudin 2018 zuwa Fadar Shugaban Kasa

Majalisar Dattawa ta mika Kasafin Kudin 2018 zuwa Fadar Shugaban Kasa

A yammacin ranar Juma'ar da ta gabata ne fadar shugaban kasa ta bayar da tabbaci na isar kasafin kudin 2018 gareta wanda majalisar dokoki ta kasa ta gabatar.

Babban hadimi na musamman ga shugaban kasa akan harkokin majilisar dattawa, Ita Enang, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban kasa da misalin karfe 8.30 na daren ranar da ta gabata.

Enang ya bayyyana cewa, ya karbi wannan kasafi a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma zai mika shi gare shi.

Shugaba Buhari yayin gabatar da Kasafin Kudin a watan Nuwamba 2017

Shugaba Buhari yayin gabatar da Kasafin Kudin a watan Nuwamba 2017

A makon da ya gabata ne majalisar dokoki ta kasa ta kammala kididdigar ta akan kasafin kudin bana kuma ta bayar da amincin ta wajen shigar da shi cikin dokar kasa bayan tsawon watanni shidda da shugaba Buhari ya gabatar da shi a farfajiyar ta.

KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Obasanjo ke fushi da Shugaba Buhari - Fadar Shugaban Kasa

A ranar Alhamis din da ta gabata ne shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya tabbatarwa da shugaba Buhari ranar mika masa kasafin kudin yayin liyafar buda baki na azumi a fadar ta shugaban kasa.

NAIJ.com ta fahimci cewa, ma'aikatar kasafi da tsare-tsaren kasa za ta shawarci shugaba Buhari dangane da sanya hannu cikin kasafin kudin domin shigar da shi cikin dokar kasa bayan ta tsarkake shi daga dukkan wasu kurakurai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An sace direbobin mota 51 a jihar Kebbi - Bagudu

An sace direbobin mota 51 a jihar Kebbi - Bagudu

An sace direbobin mota 51 a jihar Kebbi - Bagudu
NAIJ.com
Mailfire view pixel