Kungiyar matasan arewa ta goyi bayan sake zabar shugaba Buhari a matsayin shugaban kasa

Kungiyar matasan arewa ta goyi bayan sake zabar shugaba Buhari a matsayin shugaban kasa

- Kungiyar matasan arewa a ranar juma’a ta bayyana goyon bayanta ga sake zabar shugaba Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya a shekarar 2019

- Mai magan da yawun jam’iyyar Hussaini Usman, ya bayyana haka a wurin taron manema labarai a jihar Kaduna, cewa kungiyar ta yanke shawarar marawa Buhari baya ne, bayan taro da kungiyar ta gudanar a birnin tarayya a ranar 20 ga watan Mayu

- Hussaini Usman, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari, ya nuna jarumtaka wurin ciyar da Najeriya gaba musamman ta fannin tattalin arziki da kuma gine-gine na cigaban kasa

Kungiyar matasan arewa a ranar juma’a ta bayyana goyon bayanta ga sake zabar shugaba Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya a shekarar 2019.

Mai magana da yawun jam’iyyar Hussaini Usman, ya bayyana haka a wurin taron manema labarai a jihar Kaduna, cewa kungiyar ta yanke shawarar marawa Buhari baya ne, bayan taro da kungiyar ta gudanar a birnin tarayya a ranar 20 ga watan Mayu.

Kungiyar matasan arewa ta goyi bayan sake zabar shugaba Buhari a matsayin shugaban kasa
Kungiyar matasan arewa ta goyi bayan sake zabar shugaba Buhari a matsayin shugaban kasa

Hussaini Usman, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari, ya nuna jarumtaka wurin ciyar da Najeriya gaba musamman ta fannin tattalin arziki da kuma gine-gine na cigaban kasa da kuma fannin tsaro na yaki da kungiyar Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Wani yaro na kwance a asibiti bayan malaminsu na makaranta ya yi masa rauni a al’aurarsa

Usman yace dangane da wadannan abubuwan cigaba da shugaba Muhammadu Buhari, ya kawo a kasar yasa ya zama yafi kowa cancantar a zabeshi a shekarar 2019, ya kuma cancanta kowane dan Najeriya ya mara masa baya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel