Tantamar wai ko Mo Salah zai ajje azumi ranar wasan Real Madrid

Tantamar wai ko Mo Salah zai ajje azumi ranar wasan Real Madrid

- Azumi na hana a sha ruwa ko aci abinci da rana ga musulmi

- Shi kau mai azumi yakan ma saba da cewa yana azumi har yayi kwallo

- Sai dai watakil saboda uban kudin da ake bawa 'yan kwallo akan iya sanya su dole ajje azumi kar a sami tangarda

Tantamar wai ko Mo Salah zai ajje azumi ranar wasan Real Madrid
Tantamar wai ko Mo Salah zai ajje azumi ranar wasan Real Madrid

Dan wasan dan kasar Masar, wanda Musulmi ne mai bin addini sau da kafa, ya yarda da azumin watan Ramadan wanda farilla ne yinsa daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana.

Wani rahoto a shafin intanet na El-Ahly ya yi ikirarin cewar Salah zai yi azumi ranar Asabar da za a yi wasan, kuma azumi zai kai sa'a 18. Musulmin da ke Turai na yin azumi mafi tsayi idan aka kwatanta da sauran sassan duniya saboda bambancin lokaci.

DUBA WANNAN: Shugaban kasarmu makaryaci ne - Wasu Amurkawa

A baya dai, rahotanni sun nuna mutane da yawa a Turai suna sha'awar addiniin Islamma kawai saboda soyayyar su ga shi dan kwallon na shekara Mo Salah.

Moh Salah an haife shi ne a kasar Misra watau Egypt, kuma balarabe ne musulmi.

A wani labarin kuma, wasu 'yan wasan sukan nemi fatawa su ajje azumi saboda suyi wasan yayi kyau.

Idan dai azumi ya gitta da sana'ar mutum yana iya ajje wa, kamar yadda malamai suke fadi, sai dai wasan kwallo yanzu ne ya zama sana'a, a wasu wuraren kawai nishadi ne da wasa.

Addinin Islama dai ya baiwa mutane da yawa damammaki don addinin yay sauki gare su, sai dai a zamanin nan, tsatsauran ra'ayi ya sanya addinin yana gallazawa mabiansa da dokoki marasa kan-gado, wanda kan kori mutane kacokan daga addinin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel