Kasafin kudi: Ma’aikatun da su ka fi kowa rabo bana a Najeriya

Kasafin kudi: Ma’aikatun da su ka fi kowa rabo bana a Najeriya

Sai a kwanan nan ne Majalisar Tarayyar Najeriya ta amince da kasafin kudin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika gaban ta tun karshen bara. Majalisa ta kara adadin kudin da Najeriya za ta kashe a shekarar bana.

Kasafin kudi: Ma’aikatun da su ka fi kowa rabo bana a Najeriya
Shugaban kasa yana gabatar da kasafin kudi a bara

Daga cikin Ma’aikatun kasar da za su fi samun kashi mafi tsoka akwai Ma’aikatar ayyuka da lantarki da gidaje da ke karkashin jagorancin Babatunde Fashola SAN da wasu Ministoci har 2. Za dai a kashe Tiriliyan 9.1 a shekarar nan.

1. Ma’aikatar ayyuka

A kasafin bana Ma’aikatar ayyuka da gidaje da lantarki za ta samu sama da Naira Biliyan 680 a cikin kasafin wannan shekarar.

2. Ma’aikatar sufuri

Ministan sufuri Rotimi Amaechi zai tashi da fiye da rubu’in Tiriliyan a shekarar nan. Ma’aikatar sufurin za ta tashi da Biliyan 252.

KU KARANTA: Abin da ya jawo bacin lokaci a kasafin kuda

3. Ma’aikatar tsaro

Za a warewa bangaren tsaro kudi har Naira Biliyan 150 daga cikin abin da ake sa rai Najeriya za ta kashe a wannan shekarar.

4. Ma’aikatar noma

Daga cikin kasafin bana, Ministan aikin gona da raya karkara zai kashe abin da ya kusa Naira Biliyan 150 shi ma a shekarar nan.

5. Ma’aikatar Ilmi

Mallam Adamu Adamu zai tashi da sama da Biliyan 140 domin aikin Ma’aikatar sa a cikin kasafin wannan shekarar ta 2018.

An dai samu cigaba bana inda aka ware kashi 1% na abin da Najeriya ke samu domin habaka bangaren kiwon lafiya. A bana an ware makudan Biliyoyi da su ka kusa Biliyan 100 ga sha’anin lafiya a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel