2019: Duk wani mai sha'awar takara ya aijye aikinsa kafin 29 ga watan Mayu - Gwamna Ortom

2019: Duk wani mai sha'awar takara ya aijye aikinsa kafin 29 ga watan Mayu - Gwamna Ortom

- Gwamna Ortom na jihar Benue ya umurci ma'aikatan jihar masu sha'awar takara a 2019 su ajiye aikinsu

- Gwamna Ortom ya ce duk wanda bai ajiye aikinsa ba kafin 29 ga watan Mayu zai iya fuskantar hukunci

- Wasu lauyoyi sun ce umurnin gwamnan ya yi dai-dai da dokar aikin gwamnati da tayi hani ga ma'aikatan su shiga takara ba tare da ajiye aikinsu ba

A halin yanzu da ake ta shirye-shiryen tunkarar babban zaben kasa na 2019, Gwaman Samuel Ortom na jihar Benue ya umurci dukkan masu rike da mukaman siyasa da ma'aikatan gwamnati da ke sha'awar takara a zaben su ajiye ayyukansu.

Gwamna Ortom ya sallami ma'aikata da ke niyyar shiga siyasa
Gwamna Ortom ya sallami ma'aikata da ke niyyar shiga siyasa

A wata sanarwa da ta fito daga babban sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Anthony Ijohor (SAN), gwamnan ya umurci masu niyyar takarar su ajiye ayyukansu kafin ranar 29 ga watan Mayu ko kuma su fuskanci hukunci.

KU KARANTA: Daga yanzu laifi ne aurar da macen da bata haura shekaru 18 ba - Gwamnatin jihar Borno

Wani sashi na daga sanarwan ya ce: "Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya umurci dukkan masu rike da mukamman siyasa da ma'aikatan gwamnatin jihar Benue da ke sha'awar fitowa takara a zaben 2019 da su ajiye ayyukansu kafin ranar 29 ga watan Mayun 2018."

Gwamnan ya yi gargadi a kan fara yakin neman zabe kafin ajiye aiki, inda ya ce aikata hakan laifi ne da dauke da hukunci saboda saba umurnin gwamnan.

Wasu lauyoyi da suka nemi a sakayya sunayensu sun shaidawa kamfanin dillancin labaran kasa (NAN) cewa gwamnan yana da ikon gindayawa ma'aikatan ajiye ayyukansu tunda dama nada su akayi.

Sun kuma yi karin bayani da cewa dama dokar aikin gwamnati ta hana ma'aikata tsunduma hannunsu cikin takarar siyasa a yayin da suke rike da wata mukami ko aikin gwamnati.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel