Daga karshe, Jam'iyyar APC ta bayyana ranan taron gangaminta

Daga karshe, Jam'iyyar APC ta bayyana ranan taron gangaminta

Kwamitin taron gangamin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta zabi 23 ga watan Yuni a matsayin ranan da za ta gudanar da taron gangaminta sabanin 2 ga watan Yuni da aka sanar a baya.

Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, ya sanar da hakan ne a birnin tarayya, Abuja, yayinda yake rantsar da kananan kwamitoci 12 kunshe da mambobi 240 da zasu taimaka wajen gudanan taron.

KU KARANTA: Gwamnan Kwara ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 19

Kwamitocin sune na yada labarai, kudi, tantance masu zabe, tsaro, sufuri, abinci, masauki, wajen taro, lafiya da sauran su.

Yace: "An bada shawaran cewa ayi taron ranan 23 ga watan Yuni amma sai mun tattauna da sakatariyan jam'iyyar domin tabbatar da ranan,".

Shugaban kwamitin ya kara da cewa duk da cewa akwai wasu kalubale da ake fuskanta na rikice-rikicen da suka faru a jihohi, wannan ba matsala bane.

Game da cewarsa, za'a shawo kan wadannan matsaloli kafin ranan taron gangamin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar APC ta bayyana abinda za ta yi ko da za gudanar Zaɓe a yanzu

Jam'iyyar APC ta bayyana abinda za ta yi ko da za gudanar Zaɓe a yanzu

Jam'iyyar APC ta bayyana abinda za ta yi ko da za gudanar Zaɓe a yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel