Shugaban majalisar dinkin duniya ya jinjinwa shawarar da Najeriya ta yanke akan yaki da rashawa

Shugaban majalisar dinkin duniya ya jinjinwa shawarar da Najeriya ta yanke akan yaki da rashawa

- Babban Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, yayi jinjina ga matakin da Najeriya ta shirya dauka don magance rashawa

- Guterres ya bayyana haka ne a wurin taron muharawa na kungiyar da ta cika shekaru 15 da kaddamar da bikin yaki da rashawa a kasar New York

- Sakataren ya bayyana cewa cikin kokari da Najeriya tayi na magance satar kudaden gwamnati zuwa wasu kasashe yasa an mayarwa gwamnatin da kudade masu dama

A ranar 23 ga watan Mayu, 2018, a New York, babban Sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres yayi jinjina ga matakin da Najeriya ta shirya dauka don magance rashawa, yace Najeriya ta taka muhimmiyar rawa a cikin kasashen Afirika masu kokarin yaki da rashawa.

Guterres ya bayyana haka ne a wurin taron muharawa na kungiyar da ta cika shekaru 15 da kaddamar da bikin yaki da rashawa a kasar New York.

Sakataren ya bayyana cewa cikin kokari da Najeriya tayi na magance satar kudaden gwamnati zuwa wasu kasashe yasa an mayarwa gwamnatin da kudade masu dama.

Shugaban majalisar dinkin duniya ya jinjinwa shawarar da Najeriya ta yanke akan yaki da rashawa

Shugaban majalisar dinkin duniya ya jinjinwa shawarar da Najeriya ta yanke akan yaki da rashawa

Yace indai har gwamnati da gaske take tana so ta kyautatawa mutanen ta, to ta kasance mai aiwatar da ayyuka masu inganci da kuma magance rashawa kada ya kasance alqawarin siyasa kawai ko kuma abun rubutawa a jariru kawai ba.

KU KARANTA KUMA: BMO ta mayarwa kungiyar arewa martani na cewa babu makawa Buhari ya cancanci tsayawa takara a shekarar 2019

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa rashin bawa matasa maza da mata dama shine yake kara hassasa rashawa a cikin al’umma, wanda kuma hakan illa ne ga al’umma sannan kuma yana haifar da tsananin rikici a tsakanin al’umma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hari la yau: ‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi

Masu garkuwa sun sace matar wani malamin addini a Kaduna bayan sun kashe shi

Hari la yau: ‘Yan bindiga a Kaduna sun sace matar malamin addini bayan sun kashe shi
NAIJ.com
Mailfire view pixel