Shugaba Buhari ya sha suka a kan yabon Abacha

Shugaba Buhari ya sha suka a kan yabon Abacha

Wasu dandazon masu sharhi a kan siyasa sunyi tarayya wajen sukar shugaba Muhammadu Buhari bisa kalamen yabo da jinjina ta ya yi a kan tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha.

Masu sharhin siyasan sun bayyana cewa kalaman na shugaba Buhari kawai ya furta ne don ya kawar da hankalin mutane a kan muhimman abubuwa da ke faruwa a kasar yayin mabanbantan hira da sukayi da jaridar Punch.

Shugaba Buhari ya sha suka a kan yabon Abacha
Shugaba Buhari ya sha suka a kan yabon Abacha

A ranar Talata da ta gabata ne shugaba Muhammadu Buhari ya ce," Duk da irin kallon da wasu mutane ke yiwa Abacha, ya amince sunyi aiki tare kuma sunyi gine-gine tituna daga Abuja zuwa Fatakwal da Benin da Onitsa da sauransu."

KU KARANTA: Buhari ya yabi Abacha, ya ce duk abinda za a fada a kan sa, ya yi rawar gani

A yayin da ya ke shirhi kan kalaman shugaban kasan, shugaban kungiyar sa ido kan canja mulki, Dr. Abiola Akiyode-Afolabi ya yi tambaya inda ya ce, "Ta yaya wani zai yiwa Abacha jinjina? Wanda ya saci kudin gwamnati? Mai mulkin kama karya? Mai kashe mutane? Gaskiya shugaban kasa ya yi kuskure, ko mene ya sa ya furta wannan magana, ya yi ne kawai don janye hankalin mutane, mun san abinda Abacha ya aikata kuma Buhari ba zai iya canja tarihi ba."

Shi kuma wani shugaba a kungiyar Afenifere, Cif Ayo Adebanjo ya ce Buhari ya yabi Abacha ne saboda ya yi aiki karkashinsa kuma ya sami kudi a yayin mulkin kama karyar wannan lokacin.

Ya ce dama tun farko Buhari ya yi ta furta cewa Abacha ba barawo bane lokacin yakin neman zabensa duk da cewa gwamnatinsa a yanzu tana ta karbo kudaden da Abacha ya sace ya kai kasashen waje.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel