Adadin mutanen da suka mutu a Najeriya cikin wata 6 sanadiyyar hadarin mota

Adadin mutanen da suka mutu a Najeriya cikin wata 6 sanadiyyar hadarin mota

Fiye da 'yan Najeriya 2,598 suka mutu a sanadiyyar hadarin mota a tsakanin watan Oktoban shekarar 2017 zuwa watan Maris 2018, inji hukumar hasashe ta kasa wato National Bureau of Statistics (NBS) a turance

Adadin mutanen da suka mutu a Najeriya cikin wata 6 sanadiyyar hadarin mota
Adadin mutanen da suka mutu a Najeriya cikin wata 6 sanadiyyar hadarin mota
Asali: Facebook

Fiye da 'yan Najeriya 2,598 suka mutu a sanadiyyar hadarin mota a tsakanin watan Oktoban shekarar 2017 zuwa watan Maris 2018, inji hukumar hasashe ta kasa wato National Bureau of Statistics (NBS) a turance. Hukumar ta bayyana hakan a rahoton da aka dauka na hanyoyin sufuri a cikin karshen shekarar 2017, zuwa farkon shekarar 2018, wanda ta saka a shafin ta na yanar gizo.

DUBA WANNAN: Kamfanin Google zai kashe miliyan 700 a Najeriya kan kamfunna masu neman jari

Rahoton ya nuna cewa mutane 1,306 sun mutu sanadiyyar hadarin motar a karshen shekarar 2017, yayinda mutane 1,292 suka mutu a sanadiyyar hadarin motar a farkon shekarar 2018. Sai dai kuma a yanda adadin ya nuna, kamar an dan samu raguwar rasa rayukan fiye da rahoton da aka dauka a shekarar data gabata.

Bisa ga bayanan da aka dauka, ya nuna cewar mutane 2,489 suka mutu a shekarar data gabata, yayinda mutane 2,482 suka mutu a wannan shekarar. Hukumzr ta bayyana ainahin abubuwan da suke kawo asarar rayukan a hanyoyin, inda ta bayyana na farkon shekarar nan da gudu marar misali, kamar yadda ta nuna kashi 50.81 cikin 100 na yawan hadarurrukan da aka rawaito.

Rahoton ya bayyana cewar kashi 8.26 cikin 100 ya faru ne sanadiyyar fashewar taya da kuma tukin ganganci. Sannan kuma rahoton ya bayyana cewar kashi 45.8 na hadarin da ya faru a karshen shekarar 2017 ya faru ne sanadiyyar gudun gangancin.

Hukumar ta bayyana cewar kashi 10.08 na asarar rayukan ya faru ne sanadiyyar kwacewa da ababen hawan suke yi daga hannun masu tuka su.

A karshe rahoton ya nuna cewar akalla mutane 15,815 ne suka samu raunuka a sanadiyyar hadarin motar a cikin watanni shidan nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel