Wata Mata ta yanki Tikitin Shekaru 15 a gidan Kaso da laifin yiwa wani Yaro Fyade

Wata Mata ta yanki Tikitin Shekaru 15 a gidan Kaso da laifin yiwa wani Yaro Fyade

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, wata mata 'yar Kasar Kenya mai shekaru 24 a duniya, Judith Wandera, ta yanki tikitin shekaru 15 a gidan wakafi bisa aikata laifin yiwa wani yaro dan shekaru 16 fyade.

Kotu dai ta yankewa matashiyar wannan hukunci bisa laifin lalata da karamin yaron a lokuta daban-daban, yayin da shaidu da dama suka tabbatar da wannan tuhuma a gaban kotun.

Nyakundi Mukaya, Lauya mai shigar da korafi a gaban kotun ya bayar da shaida da cewa, binciken kwararrun lafiya akan mutane biyun ya tabbatar da wannan zargi na alakar daduro dake tsakanin su.

Judith Wandera

Judith Wandera

Kamar yadda rahotanni da sanadin kafar watsa labarai ta Standard Media a kasar suka bayyana, kimanin watanni hudu da suka gabata ne wannan saurayi ya fara tarayya da Misis Judith, inda ya bar gidan iyayen sa ya koma rayuwar sa tare da ita.

KARANTA KUMA: Fayemi na shirin barin Majalisar shugaba Buhari

NAIJ.com ta fahimci cewa, neman iyayen yaron akan shiga tsakaninsa da budurwar sa ya sanya hukumar 'yan sanda ta shiga cikin lamari inda ta ceto shi daga hannun wannan mata baya ga tabarbarewar harkokin karatun sa da ta yi sanadi.

Sai dai ana ta jawabin, Judith ta bayyana cewa ba ta da masaniyar karamin yaro ne inda ta ce sun hadu ne a wata mashaya wadda daga nan tarayyar su da shi ta kan kama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
APC: Muna nan muna neman hanya da wasu Sanatocin PDP don tsige Saraki

APC: Muna nan muna neman hanya da wasu Sanatocin PDP don tsige Saraki

APC: Muna nan muna neman hanya da wasu Sanatocin PDP don tsige Saraki
NAIJ.com
Mailfire view pixel