Gwamnan Kwara ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 19

Gwamnan Kwara ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 19

- Gwamna Abdulfatah ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 19 gabannin zaben 2019

- Sai dai yayi musu bayani kana cewa yan jihar babu kudi ga shi jama'a na son ayi musu aiki

- Da gwamnan da shugaban Majalisar Dattijai sun koka a makan da ya gaba kan yunkurin shafa musu kashin kaji a 'Yan sanda ke son yi.

Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed a yau Laraba ya rantsar da sababbin Kwamishinoni 19 don fara aiki.

Da yake saba musu rantsuwar Gwamna Abdulfatah ya ce, sabbin Kwamishinonin sun zo a dai-dai lokacin da jihar ke fama da matsin tattalin arziki ga kuma bukatun jama’ar jihar na kara karuwa.

Gwamnan Kwara ya rantsar da sabbin Kwamishinoni 19
Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed
Asali: Depositphotos

Sabbin Kwamishinonin da aka rantsar sun hada da: Ahaji Saidu A. Habeeb, Ma’aikatar kananan hukumomi da Mallam Ishak Mohammed Sabi, Ma’aikatar yada labarai da

Mallam Ahmed Alhassan, Ma’aikatar albarkatun kasa da Mr. Amos Sayo Justus, Ma’aikatar Muhalli da gandun Daji da Alhaji Wasiu Odewale, Ma’aikatar Tsare-tsare da cigaban tattalin arziki da Alhaji Aro Yahaya, Ma’aikatar aiyuka da sufuri.

Idan ba'a manta ba dai a cikin satin da muke ciki Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda shugaban Majalisar Datiijai Bukola Saraki yayi korafin kan irin kashin kajin da shugaban rundunar 'Yan sanda ta kasa Ibrahim Idris yake yunkurin shafa masa da shi da Gwamnan jihar tasa Abdulfatah Ahmed.

Ragowar sun hada da Suajudeen Akanbi, Ma’aikatar Gidaje da cigaban karkara da Alhaja Bilikis Oniyangi, Ma’aikatar Ilimi da Mr. Yusuf Abdulqodir, Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da Mr. Eleja Taiwo Banu, Ma’aikatar Makamashi da Ajibade Kamaldeen Adeyemi (SAN), Ma’aikatar Shari’a.

KU KARANTA: Ku tsame ni cikin batun sace Sandar Majalisa domin babu hannu na ciki - Ndume

Da kuma Ademola Nurudeen Baanu, Ma’aikatar Kudade da Mr. Agboola Julius Babatunde, Ma’aikatar Kasuwanci da Dr Ahmed Susa’ade Aminat, Ma’aikatar Al’adu da yawon bude idanu da Abdullahi Alikinla, Ma’aikatar Ililimi mai zurfi da Kimiyya da fasaha.

a cikin sabbin nadin dai akwai wakilcin bangaran Maza da kuma Mata ba kamar yadda aka saba ganin a wasu lokatan Maza ne zalla ba.

wadanda suka rage sun hada da: Alhaja Taibat Ayinde Ahmed, Ma’aikatar Harkokin Mata da Mr. Bamidele Adegoke Oladimeji, Ma’aikatar Noma da Albarkatun Kasa da Muyideen O. Alalade, Ma’aikatar Wasanni da cigaban Matasa da Alhaji Usman Kolo Rifun, Ma’aikatar Lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel