Ribar Ramadana: Wasu ‘yan mata biyu sun musulunta bayan wa’azin azumi ya ratsa su

Ribar Ramadana: Wasu ‘yan mata biyu sun musulunta bayan wa’azin azumi ya ratsa su

- A yau, Laraba, 23 ga watan Mayu day a yi daidai da 7 ga watan Ramadana wasu mata guda biyu suka musulunta a jihar Filato

- Matan sun karbi Kalmar shahada ne a wurin tafsirin Ustaz Rabi’u Musa, shugaban ‘yan agaji na jihar Filato

- Matan guda biyu; Jennifer da simi, sun canja sunayen su ya zuwa Zainab da Aisha bayan an basu Kalmar shahada

A yau, Laraba, 23 ga watan Mayu day a yi daidai da 7 ga watan Ramadana, 1439 bayan hijira, wasu mata guda biyu suka musulunta a jihar Filato a wurin tafsiri.

Matan sun karbi Kalmar shahada ne a wurin tafsirin Ustaz Rabi’u Musa, shugaban ‘yan agaji na jihar Filato kuma shughaban wata kafar sadarwar yanar gizo ta NIMC.

Matan guda biyu; Jennifer da simi, sun canja sunayen su ya zuwa Zainab da Aisha bayan an basu Kalmar shahada.

Ribar Ramadana: Wasu ‘yan mata biyu sun musulunta bayan wa’azin azumi ya ratsa su
Ribar Ramadana: Wasu ‘yan mata biyu sun musulunta bayan wa’azin azumi ya ratsa su

Ana samun yawaitar karuwar mutane dake karbar addinin Islama yayin gudanar da tafsiran watan Ramadana a wasu jihohin arewacin Najeriya.

DUBA WANNAN: Obasanjo ya lissafa halayen shugaba nagari guda 4

A wani labarin na Legit.ng, kun karanta cewar, kungiyar kiristoci ta Najeriya ta bukaci gwamnati da ta mayar da ofishin tan a jakadanci dake kasar Isra’ila daga birnin Tel Avi zuwa Jerusalem.

Shugaban kungiyar CAN, Dakta Samson Ayokunle, ne ya yi wannan kira a cikin wata takarda da mai magana da yawun sa, Adebayo Oladeji, ya fitar jiya a Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel