Har yanzu ba Mu kai ga kama wanda ya sace Sandar Majalisa ba - ‘Yan sanda

Har yanzu ba Mu kai ga kama wanda ya sace Sandar Majalisa ba - ‘Yan sanda

- Har yanzu akwai sauran rina a kaba kan Maganar kamo wanda ya dauke Sandar girma ta Majalisar Dattijai

- Wani babban Jami'in 'Dan sanda ne ya bayyana hakan ga kwamitin binciken yadda aka sace Sandar Majalisar

Kwamishinan ‘Yan sandan Abuja Habu Sani, ya fadawa kwamitin Majalisar Dattaijai dake binciken yadda aka sace Sandar Majalisar cewa har yanzu rundunar ‘Yan sanda ba ta kai ga kama wanda ya dauki Sandar ba, duk kuwa da cewa sun kama Mutane 6 da ake zargi.

Har yanzu ba Mu kai ga kama wanda ya sace Sandar Majalisa ba - ‘Yan sanda
Har yanzu ba Mu kai ga kama wanda ya sace Sandar Majalisa ba - ‘Yan sanda

Legit.ng dai ta rawaito muku yadda wasu Matasa suka kutsa kai cikin Majalisar har kuma su kayi awon gaba da Sandar ikon.

Jim kadan bayan faruwar hakan ne ‘Yan sandan suka bayyana cewa sun samu nasarar damke wasu Mutane 6 da ake zargin su suka aikata baranbaramar, amma ciki babu wanda ya sanya hannu ya dauki sandar.

Yayin binciken shugaban kwamitin binciken Sanata Bala Na’Allah ya fara ne da ganin baiken yadda ‘Yan sanda suka mayar da wadanda ake zargin babbar shelkwatar tsaro bayan kuma an kama su ne a Ofishin shiyya.

KU KARANTA: Ana rikici akan kujerun ‘yan majalisa da suka rasu akan mulki

Bayan saba rantsuwar fadar gaskiya yayin amsa tambayoyin, Kwamishinan ‘Yan sandan ya bayyana musu cewa a tare da wadanda aka kama an samu wayoyin hannu biyu da wasu layoyi biyu da katin shaida aiki a Gidan Gwamnatin jihar Kogi da kuma takardar mannawa ta Gidauniyar tallafawa Mata ta jihar Kogi da sauransu.

Kwamishinan ya shaida musu cewa a ranar da abin ya faru sun mayar da hankali ne wurin kama wadanda ake zargin, sai dai kuma kash sai ga umarni daga babbar shelkwatar tsaro sun don zo tafiya da wanda ake tunanin shi ya zo da ‘yan daban Sanata Omo Agege, sai suka hada har da wadanda muka kama suka tafi da su. Kuma har ya zuwa yanzu ba su ma samu ganawa da su wadanda ake zargin ba.

Har yanzu ba Mu kai ga kama wanda ya sace Sandar Majalisa ba - ‘Yan sanda
Har yanzu ba Mu kai ga kama wanda ya sace Sandar Majalisa ba - ‘Yan sanda

Fadin wannan magana na rashin ganawa da Mutanen da ake zargin da Kwamishinan yayi ne ya harzuka Sanatocin matuka wani guda daga cikinsu mai suna Betty Apiafi ya bayyana shakkunsa ko za su iya gudanar da binciken cikin lokacin da ake da bukata kuma a samu nasara

Sai kwamishinan ya amsa da cewa “Ai wannan shi ne babban dalilin da yasa muke da bukatar Kyamarorin tsaron (CCTV) domin da dasu da tuni ba’a zo ga wannan matakin na turjiya da kin amsa laifi ba.”

Daga nan Sanata Bala Na’Allah ya ce da Kwamishina Sani su shaidawa jami’an da suke kula da batun satar Sandar a can shelkwatar tsaro da su hallara yau Laraba da safe a gaban kwamitin binciken domin amsa tambayoyi.

Kana Sanatan ya ce bai kamata ‘Yan sandan su cigaba da tsare wadanda ake zargi sma awanni 24h ba tare da kais u Kotu ba.

Kuma yadda ‘Yan sandan suka gudanar da bincikensu shi zai tabbatar da hannunsu a ciki satar Sandar ko akasin haka.

A karshen Kwamishinan ya mika musu rahoton farko da ‘Yan sandan suka hada kan binciken taree da basu tabbacin ba zai bari ‘yan Jarida su gani ba balle a fara tsegumi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel