Hukumar EFCC za ta gurfanar da Shekarau da Wali a ranar Alhamis

Hukumar EFCC za ta gurfanar da Shekarau da Wali a ranar Alhamis

A ranar Alhamis, 24 ga watan Mayu za’a gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau tare da Ambassador Aminu Wali da kuma injiniya Mansur Ahmed a gaban kotun tarayya dake Kano kan zargin handame kudade N950m na yakin neman zabe.

Lauyan dake kare manyan mutanen uku, Barista Abdul Adamu Fagge, ya bayyanawa manema labarai a jiya a Kano cewa hukumar EFCC tana tuhumarsu akan handame wasu kudade.

Fagge yace tuhuma na farko da biyu ya fada akan Shekarau da Wali kan karban N25m ko wannensu cikin N950m, yayinda na ukun ke kan Injiniya Ahmed wanda ake zargin ya karbi N10m.

Tuhuma na hudu na kan Wali kan karban N950m, na biyar akan Shekaru da Wali kan ajiye N950m a gidan tsohon gwamnan jihar Kanon sannan kuma na shida na akansu su uku ne ha hada kai wajen karban kudin.

Hukumar EFCC za ta gurfanar da Shekarau da Wali a ranar Alhamis
Hukumar EFCC za ta gurfanar da Shekarau da Wali a ranar Alhamis

Shekarau da Wali sun isa ofishin EFCC na Kano cikin mata kirar Peaugeot 406 kalar toka da lamba ABC 990 PQ da misalin karfe 3:15 na rana cikin tawagar magoya bayansu a harkar siyasa.

KU KARANTA KUMA: Sake zabar Buhari shine abu mafi sauki – Lai Mohammed

Idan baza ku manta ba a watan Mayun 2016 hukumar yaki da rashawa ta gayyaci manyan yan nsiyasan uku bisa zargin raba mu kashe da na kudi N950m da suka yi a gidan Shekarau.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel