Matasa ci ma zaune: Buhari ma ci ma kwance ne – Inji wani Dan Najeriya da ya ji jiki

Matasa ci ma zaune: Buhari ma ci ma kwance ne – Inji wani Dan Najeriya da ya ji jiki

Wani mutumi da ya shahara wajen barkwanci a jihar Kano da ake yi ma suna Taliya ya bayyana wahalar da ake ciki a wannan zamani na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a cewarsa ta kai intiha, kamar yadda gidna talabijin na Dokin Karfe ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito bidiyon wannan bawan Allah ya samu karbu a hannun ma’abota shafukan sadarwar zamani, musamman yadda yake nishadantar da jama’a ta hanyar dangantasu da halin matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar.

KU KARANTA: Buhari ya yi gaskiyar, Obasanjo ne silar tabarbarewa wuta a Najeriya – Atiku Abubakar

Taliya ya kalubalanci shugaba Buhari da ya bayyana ma yan Najeriya nawa ya ci a jinya da ya kwashe tsawon lokaci yana yi a Asibitin birnin Landan, inda yace idan Buhari ya bayyana yan Najeriy a matsayin ci ma zaune, toh shi kuma ci ma kwance ne.

Sai dai wannan mutumi yayi korafin cewa ya tura ma shugaban kasa Muhammadu Buhari gudunmuwar naira hamsin a yayin yakin neman zabensa na takarar shugaban kasa a shekarar 2015, amma yace har yanzu bata dawo ba, babu uwa babu riba kenan.

Mutumin ya yi mamakin yadda ace shugaba Buhari har kuka ya yi kafin zabe, amma ace a yanzu jama’a na kokawa da salon kamun ludayinsa? Don haka yake ganin dama can ashe Mage ce mai kwanciyar daukan rai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel