Gwamnatin jihar Gombe ta girgiza a sanadiyyar mutuwa da ta rutsa da wani babban jami’inta

Gwamnatin jihar Gombe ta girgiza a sanadiyyar mutuwa da ta rutsa da wani babban jami’inta

Babban lauya, kuma kwamishinan shari’a na jihar Gombe, Abdulhameed Ibrahim ya gamu da ajalinsa a ranar Talata 22 ga watan Mayu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wani na kusa da iyalan mamacin ya tabbatar da mutuwarsa, inda yace kwamishinan ya rasu yana da shekaru 58, kuma ya rasu ne da ranar Talata a wani Asibiti mai zamansa kansa dake kasar Indiya, inji rahoton majiyar NAIJ.com.

KU KARANTA: Zargin ɓarnatar da dala biliyan 16: Babu abinda ka sani – Obasanjo ga Buhari

Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ne ya nada Marigayin mukamin kwamishinan sharia a shekarar 2011, sai dai kafin nan sun yi aiki tare da gwamnan a ma’aikatu daban daban.

Gwamnatin jihar Gombe ta girgiza a sanadiyyar mutuwa da ta rutsa da wani babban jami’inta

Abdulhameed

Abdulhameed ya taba rike mukamin mataimakin darakta a gidan rediyon tarayya, FRCN, sai kuma sakataren sharia na kamfanin Siga na Savannah dake jihar Adamawa, shugaban karamar hukumar Akko, mataimakin Darakta a ma’aikatar sharia ta tarayya, haka zalika yayi aiki a ofishin sakataren gwamnati.

Daga karshe sanarwar mutuwar tasa ta karkare da cewa mamacin ya mutu ya bar yara goma da mata biyu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
2019: Matsaloli 3 da Jam'iyyar PDP za ta fuskanta yayin Zaben fitar da gwani

2019: Matsaloli 3 da Jam'iyyar PDP za ta fuskanta yayin Zaben fitar da gwani

2019: Matsaloli 3 da Jam'iyyar PDP za ta fuskanta yayin Zaben fitar da gwani
NAIJ.com
Mailfire view pixel