Raddi: Shirya nike da binciken da Buhari yace zai yi a kaina - Obasanjo

Raddi: Shirya nike da binciken da Buhari yace zai yi a kaina - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya mayar da martani da shugaba Muhammadu Buhari akan zargin almubazzarancin $16 billion kan samar da wutan lantarki.

A wani jawabin ya mai magana da yawun Obasanjo, Kehinde Akinyemi, ya saki, ya ce shugaba Muhammadu Buhari yayi magana a kan jahilci.

Yayinda ya karbi bakuncin magoya bayansa a fadar shugaban kasa a yau Talata, shugaba Buhari yace tsohon shugaban kasa ya amsa tambayoyi a kan kudaden.

Raddi: Shirya nike da binciken da Buhari yace zai yi a kaina - Obasanjo

Raddi: Shirya nike da binciken da Buhari yace zai yi a kaina - Obasanjo

Amma a raddinsa, tsohon shugaba Obasanjo yace: "Amsan abu ne mai sauki; wutan lantarkin na cikin ayyukan bunkasa wutan lantarki 7 da kuma na'urorin gas 18..."

Ya bukaci shugaba Buhari ya karanta littafinsa mai suna 'My Watch' wanda ya wallafa saboda duk yayi wadannan bayanai a ciki.

KU KARANTA: Maganganu masu zafi da Shugaba Buhari ya furta yau Talata

Yace idan kuma Buhari bai iya karatu ba, ya umurci hadimansa da su tayashi karantawa da kuma yi masa bayanin da zai fahimta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Babban sufetan Yansanda ya canza ma rundunar Yansandan SARS suna, karanta

Sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel