Maganganu masu zafi da Shugaba Buhari ya furta yau Talata

Maganganu masu zafi da Shugaba Buhari ya furta yau Talata

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa bisa yadda shugabannin da suka gabata suka rika almubazzaranci da dikiyar kasa

- Yayi maganar ne cikin kalaman da suke kama da gugaar zana ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari furta kalamai masu zafi ga Barayin shugabnnin Najeriya da suka yiwa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa ta hanyar sama da fadi da kudin samar da wutar lantarki da rufda ciki kan kudaden haraji da kuma sace kudin Man fetur da cewa makiya ne ga kasar nan.

Maganganu masu zafi da Shugaba Buhari ya furta yau Talata
Maganganu masu zafi da Shugaba Buhari ya furta yau Talata

Muhammadu Buhari yayi wadannan kausasan kalamai ne yayinda ya karbi bakuncin wata kungiya mai goyon bayansa mai suna Buhari Support Organisations (BSO) karkashin jagorancin shugaban hukumar Kwastam ta kasa Col. Hameed Ali, a fadar shi dake Villa a Abuja.

Buhari ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su kasance masu lura sosai wajen zabar wadanda zasu ja ragamar shugabanci a kowanne mataki a kasar nan duba da karatowar zaben 2019.

“Na kalubalanci duk kowa da duba sauran Nahiyoyin Europe, America and Asia a dan tsakanin shekarun 1999 zuwa 2014, Najeriya na fitar da gangar mai Miliyan 2.1m akan farshin $100 zuwa $143 gagan guda.

Amma lokacin da mu ka hau mulki ya karye raga-raga zuwa 37-38 ganga guda daga baya ya fara dagawa zuwa $40-50.”

KU KARANTA: Mun shirya tsaf don farfado da Jirgin saman Najeriya nan da ‘yan watanni – Gwamnatin tarayya

Muhammadu Buhari ya cigaba da cewa, “Nan take na garzayi wurin gwamnan babban banki ko muna da kudi, ya ce min ai sai dai ma bashi da ake binmu.”

Maganganu masu zafi da Shugaba Buhari ya furta yau Talata
Maganganu masu zafi da Shugaba Buhari ya furta yau Talata

Shugaban ya kuma nuna bacin ransa bisa yadda wasu shugabannin da suka gabata suka nakasa tattalin arzikin kasar nan, inda ya bayar da misalin yadda aka kashe zunzurutun kudin har $15b wajen samar da wutar lantarki wadda ga shi kuma har yanzu bata samu ba.

Buhari ya kuma ce a cikin kasafin kudin shekarar 2016 da 2017 kasar nan ta mori kaso mafi tsoka (N2.8tr) da ba’a taba ware irin ga gudanar da manyan aiyuka ba a tarihin Najeriya ba cikin shekara biyu kacal.

A don haka ne shugaban yayi kira ga ‘yan Najeriya da su kujewa duk wani abu da zai jawowa kasar nan farraku musamman rigimar addini da kabilanci domin basa kawo komai face ci baya.

Daga kashe Buhari ya godewa kungiyar bisa irin taimako da goyon bayan da suke ba shi.

Anan shi jawabin Hameed Ali cewa yayi, mafi yawan ‘yan Najeriya suna goyon bayan sake tsayawa takararsa shugaba Buharin a karo na biyu sakamakon kishin kasa da gaskiyarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel