Yanzu-yanzu: An damke yan fashin bankin Offa da ake nema ruwa a jallo

Yanzu-yanzu: An damke yan fashin bankin Offa da ake nema ruwa a jallo

Hukumar yan sandan Najeriya ta cika hannu da yan fashi da makami da suka hallaka akalla mutane 30 a fashin bankuna a karamar hukumar Offa, jihar Kwara kwanakin bayan sun shiga hannu.

Hukumar ta saki wannan labari ne da yammacin yau Litinin, 21 ga watan Mayu, 2018 ta shafin ra'ayi da sada zumuntarta na Facebook.

Yanzu-yanzu: An damke yan fashin bankin Offa da ake nema ruwa a jallo

Yanzu-yanzu: An damke yan fashin bankin Offa da ake nema ruwa a jallo

Jawabin yace: "Bisa ga wallafa hotunan yan fashin bankuna a Offa, muna samun labaran leken asiri daga jama'a kuma jami'an tsaronmu da aka tura Kwara, Ondo, Osun, da Ekiti sun samu nasarar damke 2 daga cikin yan fashin.

Yan fashin sune Kunle Ogunleye, dan shekara 35 ya shiga hannu ne jiya a garin Oro, jihar Kwara. Na biyu shine Micheal Adikwu, dan jihar Kwara wanda ya kasance jami'in dan sanda kafin hukumar ta sallamesa a shekaran 2012. An jefa kurkukun shekara 3.

Bayan shekaru ukun, ya fito a 2015 kuma ya zama tantirin dan fashi da makami. An damke shi ne a jihar Kwara makonni biyu da suka gabata.

Wadanda suka shiga hannu yanzu suna taimakawa hukuma wajen cigaba da gudanar da bincike."

KU KARANTA: Na dawo da karfi na kuma zan kuma cigaba da gwagwarmaya - Melaye

NAIJ.com ta kawo muku rahoton cewa hukumar yan sanda ta wallafa hotunan yan fashin da suka kai mumunan hari kimanin bankuna 4 a jihar Kwara inda suka kashe jama'a ba gaira ba dalili.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa

Dalilin da ya sanya muke so Buhari ya zarce har bayan 2019 Inji wani Gwamna a Arewa
NAIJ.com
Mailfire view pixel