Yanzu-yanzu: Olisa Metuh ya yanke jiki ya sume a kotu

Yanzu-yanzu: Olisa Metuh ya yanke jiki ya sume a kotu

Tsohon kakakin jam’iyyar PDP, Cif Olisa Metuh, ya yanke jiki ya fadi warwas da safen nan yayinda za’a gurfanar da shi gaban babban kotun tarayya da ke Abuja.

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC tana tuhumar Metuh da kamfaninsa Destra Investment Limited, da laifin amsan kudi N400m daga hannun tsohon NSA, Sambo Dasuki, a shekarar 2014.

Wanda abu ya faru ne misalin karfe 9:01 na safiyan nan a cikin zauren kotun. Metuh ya kasance yana zaune a cikin kotu gaban alkalin kotun, Jastis Okong Abang.

A yanzu haka, an dakatad da karan kuma an kirayi jami’an kiwon lafiya su kula da shi. Misalin karfe 9:19, likitocin suk iso. Har yanzu jami’an lafiya na duba shi.

Yanzu-yanzu: Olisa Metuh ya yanke jiki ya sume a kotu

Yanzu-yanzu: Olisa Metuh ya yanke jiki ya sume a kotu

NAIJ.com ta kawo muku rahoton cewa wata kotun daukaka kara mallakin gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Abuja ta sha alwashin sai ta garkame tsohon kakakin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a takaice watau Olisa Metuh idan dai har bai gurfana a gaban ta ba ranar 5 ga watan Fabrairun shekarar nan.

Babban alkalin kotun ne dai mai shari'a Okon Abang ya sanar da hakan yayin da yake yanke hukunci game da uzurin da shi Olisa Metuh din ya gabatar ma kotun yana bukatar a sake daga shari'ar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jam'iyyar APC ta bayyana abinda za ta yi ko da za gudanar Zaɓe a yanzu

Jam'iyyar APC ta bayyana abinda za ta yi ko da za gudanar Zaɓe a yanzu

Jam'iyyar APC ta bayyana abinda za ta yi ko da za gudanar Zaɓe a yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel