Babban burina a Duniya – Aliko Dangote

Babban burina a Duniya – Aliko Dangote

Aliko Dangote, Biloniya dan kasuwa, ya ce babban burin sa shine ya zama babban mai tallafawa jama’a a nahiyar Afrika.

Dangote ya bayyana haka ne a karshen satin nan yayin bude wata gidauniya da rukunin kamfanonin sat a kafa a jihar Neja.

Gidauniyar, kamar yadda aka bayyana, zata tallafawa masu karamin karfi 25,000 a jihar Neja da Naira N10,000 domin bunkasa sana’o’in cikin gida.

Da yake jawabi yayin bude gidauniyar a dakin taro na Legbo Kutigi dake Minna, babban birnin jihar Neja, y ace gidauniyar sat a ware kudi biliyan N10bn domin taimako mata marasa galihu a kananan hukumomin Najeriya 774.

Babban burina a Duniya – Aliko Dangote
Aliko Dangote

Na fi son a sanni a matsayin mutumin day a fi kowa taimakon jama’a a Afrika, ba mai mutumin day a fi kowa kudi ba,” a cewar Dangote.

Sannan ya kara da cewa, “zan cigaba da amfani da dukiya da kuma murya ta domin inganta rayuwa a Najeriya da ma Afrika baki daya.”

DUBA WANNAN: Kyautar kudin shugaba Buhari ta farraka shugabannin kungiyar CAN ta Kiristoci

Dangote ya kara da cewar, gidauniyar sa ta raba adadin kudi biliyan N2.5bn ga mata marasa karfi 256,500 a jihohin Kano, Legas, Jigawa, Kogi, Adamawa, Borno da Yobe.

Babbar Darekar gidauniyar Dangote, Halima Aliko Dangote, ta bayyana cewar burin gidauniyar shine tsamo mata daga halin ni-‘ya-su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel