Zaben shugabannin APC: Sanata A'isha Alhassan tasha ruwan duwatsu

Zaben shugabannin APC: Sanata A'isha Alhassan tasha ruwan duwatsu

Da alama dai zabukan shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress, APC da ya gudana a mataki na mazabu, kananan hukumomi da kuma jahohin kasar nan na cigaba da kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin 'ya'yan jam'iyyun.

Kamar dai a jahohi da dama, a jihar Taraba ba mafusanatan matasa sun farfasa tayoyin motar babbar ministan mata a gwamnatin shugaba Buhari kuma tsohuwar 'yar takarar kujerar Gwamnan jihar ta Taraba watau Sanata Ai'sha Alhassan.

Zaben shugabannin APC: Sanata A'isha Alhassan tasha ruwan duwatsu

Zaben shugabannin APC: Sanata A'isha Alhassan tasha ruwan duwatsu

KU KARANTA: Jami'an tsaro a Najeriya sun kama Yahudawa 70

NAIJ.com ta samu cewa rahotanni daga jihar Taraba sun rawaito cewa an farfasa tayoyin motar ministar harkokin mata Hajiya Aisha Jummai Alhassan a yayin rikicin da ya barke tsakanin bangaren jam'iyyar APC wanda take jagoranta a jihar da kuma bangaren wadanda ke adawa da su.

Majiyarmu ta rawaito cewa rikicin ya barke ne biyo bayan jagorantar magoya bayanta da ministar ta yi zuwa wurin da dayan bangaren jam'iyyar APCn ke gudanar da zabe.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo

Babban sufetan Yansanda ya canza ma rundunar Yansandan SARS suna, karanta

Sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo
NAIJ.com
Mailfire view pixel