Tsoffin Gwamnoni da Mataimakansu 21 da suke karbar Albashi har sau biyu

Tsoffin Gwamnoni da Mataimakansu 21 da suke karbar Albashi har sau biyu

A kalla tsofaffin gwamnoni da mataimakan gwamnoni 21 ne a yanzu haka suke karbar albashi har rubi biyu, a matsayinsu na tsoffin gwamnoni ko Mataimakan gwamna bayan sun sauka, da kuma albashinsu na yanzu a matsayin ‘Yan Majalisar tarayya ko Minista a gwamnatin Buhari.

Shugaban Cibiyar shugabanci da cigaban al'umma Mrs Victoria Ose Udoh ta shaida bayyana cewa wasu tsofaffin gwamnoni da Mataimakansu na karbar albashi rubi biyu, ta bayyana hakan ne yayin gudanar da wani taron karawa juna sani da aka gudanar a Otal din Regview dake Kaduna a jiya Alhamis, kan albashi da alawus masu gwabi da ‘yan Majalisar ke karba.

Asirin tsoffin Gwamnoni da Mataimakansu 21 ya tonu kan yadda suke karbar Albashi har yanzu, bayan kuma suna Sanatoci ko Ministoci a gwamnatin Buhari
Asirin tsoffin Gwamnoni da Mataimakansu 21 ya tonu kan yadda suke karbar Albashi har yanzu, bayan kuma suna Sanatoci ko Ministoci a gwamnatin Buhari

Ta ce daga cikin wadanda suke karbar albashin har rubi biyu sun hada da: shugaban Majalisar Dattijai Abubakar Bukola Saraki (amma a kwanan baya ya nemi a dakatar) da tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Goodwill Akpabio da Theodore Orji da Abdullahi Adamu da Sam Egwu da Shaaba Lafiagi, da Joshua Dariye da kuma Jonah Jang tsohon gwamnan jihar Plteau.

Haka zalika tsohon gwamnan jihar Zamfara Ahmed Sani Yarima da Danjuma Goje da Bukar Abba, da Adamu Aliero da George Akume da Miss Biodun Olujimi da Enyinaya Abaribe da Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi da Chris Ngige kuma Babatunde Fashola.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta taso keyar wani na hannun daman Bukola Saraki

Da take bayyan misalin irin yadda tsofaffin masu mulkin ke sharbar riba biyu a jahohinsu ta ce, kamar a jihar Legas bayan Gwamna ya sauka za’a siya amsa gida daya a Legas da kuma a Abuja da darajarsa ta kai N500m zuwa N700m, sannan duk bayan shekaru biyu za’a biya shi kashi 300% na albashinsa a lokacin yana gwamna da kuma karin N2.5m kudin Fansho da dai sauransu.

A jihar Rivers kuwa ana bawa Gwamna ne gida guda a duk inda yake so a Najeriya yayin da mataimakinshi kuma za’a bashi gidan a duk inda yake so a fadin jihar. Sannan kuma a basu kaso 300% na albashinsu a lokacin suna kan mulki.

Akwa Ibom kuwa dokar ta baiwa tsoffin masu mulkin damar karbar har Naira N200m da gida mai daki 6 da tafiya hutu na tsawon kwanki 30 a ciki da wajen kasar nan. Haka wannan tsari yake a jihar Kano amma sai dai suna bayar da kashi dari ne na albashi yayin da masu mulkin suke kan karaga.

A jihar Gombe kuwa, tsoffin masu mulkin suna karbar N300m ne yayin da jihar Kwara ita ma take bayar da kaso 300% na albashin tare da karin ma’aikata masu yi musu hidima 5.

Sokoto kuwa suna bayar da N200m ne ga tsohon gwamnan jihar.

Victoria ta kara da cewa “ya zama dole ne a yabawa Sanata Shehu Sani sakamakon bayyana yadda gwabin albashin Sanatocin yake a karon farko tun 1999 da ake Dimukuradiyya”

Asirin tsoffin Gwamnoni da Mataimakansu 21 ya tonu kan yadda suke karbar Albashi har yanzu, bayan kuma suna Sanatoci ko Ministoci a gwamnatin Buhari
Sanata Shehu Sani- Kaduna

Duk kuwa da cewa ma’aikata a kasar nan na fama da wahala a dalilin rashin biyansu albashinsu da kuma kunci da Talakawa suke ciki sakamakon matsin tattalin arziki.

Ana shi jawabin yayin gabatar da mukalarsa babban bako mai jawabi Chibuzor Okereke cewa yayi, duk da yake ba laifin tsoffin gwamnonin ba ne, sakamakon su tasu ta kare amma tabbas ya kamata su yi tunani domin yin abinda ya dace.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel