Wasu zakakuran likitoci a jihar Adamawa sun raba wasu jarirai 2 da suka zo Duniya a hade

Wasu zakakuran likitoci a jihar Adamawa sun raba wasu jarirai 2 da suka zo Duniya a hade

Likitoci a cibiyar magani ta gwamnatin tarayya dake garin Yola na jihar Adamawa sun samu nasarar ceto rayuwar wasu jarirai yan biyu da aaka haifesu suna manne da juna, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban Asibitin, Farfesa Auwal Muhammed ne ya sanar da haka a wani taron manema labaru da cibiyar ta shirya a garin Yola, inda yace hadakar kwararrun Likitoci ne suka gudanar da aikin.

KU KARANTA:

“Mun samu nasarar raba wasu jarirai mata yan biyu da suka zo Duniya a hade a ranar 14 ga watan Mayu, kwararrun likitoci daban daban ne suka bada gudunmuwa waje ceto rayuwar jariran, kuma yaran suna cikin koshin lafiya a yanzu.” Inji shi.

Wasu zakakuran likitoci a jihar Adamawa sun raba wasu jarirai 2 da suka zo Duniya a hade
Wasu jarirai a hade

Farfesa Auwal yace likitoci sun dauki awanni hudu suna karakaina akan jariran har sai da Allah ya basu nasara, ya kara da cewa wannan aikin shi ne irinsa na biyu da asibitin ta taba gudanarwa, inda yace an yi na farkon ne a shekarar 2014, kuma shi ma an samu nasara.

Daga karshe Farfesa Auwal ya tabbatar da hazakar likitocin Najeriya, inda yace ya kamata manyan mutane a Najeriya su rage fita zuwa Asibitocin kasashen waje, saboda kasar Najeriya za ta iya yin gogayya da sauran kasashe a fannin samun kwararrun likitoci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel