Dalilin da yasa Ganduje ke min bita da kulli - Bibi Faruk

Dalilin da yasa Ganduje ke min bita da kulli - Bibi Faruk

Tsohon kwamishinan kasa na jihar Kano, Alhaji Farouk Bibi Farouk ya ce an gurfanar da shi a kotu ne saboda ya ki bayar da hadin kai wajen cin hanci da ya janyo rikicin da ke faruwa a jami'iyyar APC na jihar Kano.

Bibi Farouk ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan kotu da dakatar da shari'arsa tare da wasu mutane biyu har sai an ga hukuncin da kotun daukaka kara na jihar Kaduna ta zartar.

Dalilin da yasa Ganduje ke min bita da kulli - Bibi Faruk
Dalilin da yasa Ganduje ke min bita da kulli - Bibi Faruk

A cewarsa, gwamna Abdullahi Ganduje yana son ya muzanta shi ne saboda ya yi riko da gaskiya da rikon amana.

KU KARANTA: Abinda Buhari ya fadawa Tinubu, Osinbajo, da Oyegun a kan zaben jihar Ekiti

"A ranar 26 ga watan Fabrairun 2016, gwamna Ganduje ya umurce ni tare da wasu kwamishinoni 8 da mu rika ware N10 miliyan daga ma'aikatun mu wanda za mu mika don lokacin da bukatar hakan ta taso. Daga wannan lokacin ne gwamnatin ta fara yi min bita da kulli har ta kai ga an gurfanar da ni a kotu bisa laifin da ban aikata ba. Rashin bayar da hadin kai wajen ruruta rikicin APC a jihar Kano yana daga cikin laifufukan da nayi wa gwamnatin Ganduje," inji Farouk.

Ya kara da cewa babu wata wahala ko barazana da za'ayi masa wanda zata sanya ya tsoma hannun sa cikin wata tafiyar siyasa da baya ra'ayi.

Lauyan mai kare Bibi Farouk, Barrister Sa'id Muhammad Tudun Wada ya shaidawa Daily Trust cewa sun shigar da takardan daukaka kara a wata kotun jihar Kaduna inda suke bukatar kotun tayi musu fashin baki kan tuhume-tuhumen da ake zargin wanda ya ke karewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel