Wata amarya ta sha bulala 75 saboda tayi aure babu yardar mahaifin ta

Wata amarya ta sha bulala 75 saboda tayi aure babu yardar mahaifin ta

- Kotu ta yankewa wata amarya hukuncin bulala 75 saboda tayi aure babu ba da yardar mahaifin ta ba

- 'Yan sanda a kasar Sudan sun yiwa wata mata bulala 75 bayan kotu ta same ta da laifin yin aure ba tare da amincewar mahaifinta ba

- Matar ta zauna da mijin ta na tsawon shekara guda kafin daga bisani dangin ta su maka ta a kotu bisa zama da namiji ba bisa tsarin shari'ar Musulunci ba

Kotu ta yankewa wata amarya hukuncin bulala 75 saboda tayi aure babu ba da yardar mahaifin ta ba

'Yan sanda a kasar Sudan sun yiwa wata mata bulala 75 bayan kotu ta same ta da laifin yin aure ba tare da amincewar mahaifinta ba.

Matar, 'yar asalin yankin Dafur mai fama da yaki, an yi mata bulalar ne a ofishin 'yan sanda na Omdurman dake Khartoum, bayan ta shafe watanni shida a gidan yari.

Wata amarya ta sha bulala 75 saboda tayi aure babu yardar mahaifin ta
Wata amarya ta sha bulala 75 saboda tayi aure babu yardar mahaifin ta

Wannan hukunci na zuwa ne bayan wata kotun Sudan din ta yankewa wata matashiya hukuncin kisa saboda ta kashe mijinta bayan ya tilasta mata kwanciya da shi.

Lauyan matar, Azza Mohamed, ya ce, "a yau ne ta gama wa'adin ta na zaman gidan yari sannan kuma aka yi mata bulala 75," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

An gurfanar da matar gaban kotu ne saboda ta auri mutumin da take so duk da mahaifin ta bai aminta da shi ba.

DUBA WANNAN: Matashi mai shekaru 24 ya burmawa budurwar sa mai shekaru 19 wuka

Matar ta zauna da mijin ta na tsawon shekara guda kafin daga bisani dangin ta su maka ta a kotu bisa zama da namiji ba bisa tsarin shari'ar Musulunci ba.

Da yake bayyana takaicin sa, mamba a wata kungiyar kare 'yancin mata, Tahani Abbas, ya ce, "a hannuna na rike jaririyar ta mai wata biyu a duniya a lokacin da za a yi mata bulala."

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International tayi alla-wadai da danne hakkin mata da sunan addini da hukumomi ke yi a kasar Sudan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel