'Dan wani tsohon shugaban kasa ya aikata kuruciyar bera, ya fuskanci fushin alkali

'Dan wani tsohon shugaban kasa ya aikata kuruciyar bera, ya fuskanci fushin alkali

- An garkame dan tsohon shugaban kasa Frederick Chiluba saboda samun sa da laifin satan wayar salula

- Wata kotun majistare ne ta yanke wa Fredrick hukuncin watanni takwas tare da horo mai tsanani a gidan wakafi

- 'Dan tsohon shugaban kasar wanda tsohon jami'an hukumar sojin sama na kasar Zambia ne ya saci wayar wata Brenda Chisha ne

A yau Laraba ne wata kotun majistare da ke zamanta a Lusaka ta yanke wa dan tsohon shugaban kasar Zambia Fredrick Chiluba hukuncin zaman gidan wakafi na watanni 8 bayan an same shi da laifin satar wayar salula kamar yadda Lusaka Times ta ruwaito.

Legit.ng ta gano cewa dan shugaban kasar mai shekaru 34 a duniya yana fuskantar laifi guda daya ne na sata inda ya saci wayar wata mace mai suna Brenda Chisha.

'Dan wani tsohon shugaban kasa ya aikata kuruciyar bera, ya fuskanci fushin alkali
'Dan wani tsohon shugaban kasa ya aikata kuruciyar bera, ya fuskanci fushin alkali

KU KARANTA: Ana cigaba da musayar yawu tsakanin magoya bayan Buhari da na Atiku bayan a kan wata bukata

Fredrick Chiluba Jnr dai tsohon jami'in hukumar sojan saman kasar ta Zambia ne kuma ya saci wayar kirar Samsung S7 edge ne a shekarar 2017 kuma ya yi musayar wayar don a bashi miyagun kwayoyi a ranar 2 ga watan Satumban 2017 a garin Chibolya.

An kiyasta darajar wayar ya kai K8,500.

A shedar da ta bawa kotu, Chisha ta fadawa kotu cewa ta hadu da Chiluba ne a Woodlands a ranar 2 ga watan Satumban shekarar 2017 inda ya bukaci ta bashi aron wayar don ya yi kira.

Chisha ta cigaba da cewa "Chiluba ya bukaci ta bashi aron wayarta don ya yi kira inda na mika masa kuma bayan minti biyu ya dawo mata dashi. Bayan misalin minti goma kuma ya sake karbar wayar amma sai ya sulale ya gudu da wayar. Hakan yasa na umurci Isaac wanda abin ya faru a idonsa ya karbo min wayata.

"An kama shi a ranar Lahadi inda aka kai shi caji ofis da ke Kabwata. Na tambayeshi ya bani wayata amma sai ya ce ya manta da wayar a wani wuri. A ranar kawu na ya yi allawarin siya min wata sabuwar wayan," inji Chisha.

Alkalin kotun Nthandose Chalaba ta ce ta yanke masa hukuncin ne saboda ya zama darasi a gareshi da saura masu niyyar aikata irin abin da ya aikata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel