Kungiyar Boko Haram sun bulo da wani sabon salo na kai harin kunar bakin wake

Kungiyar Boko Haram sun bulo da wani sabon salo na kai harin kunar bakin wake

- Hukumar sojojin Najeriya tace harin da aka kai a ranar Talata wanda yayi sanadiyar rayukan jami’an tsaro na kato da gora uku a Konduga, sunyi nasara ne ta hanyar amfani da wani dattijo wanda yayi shiga ta matafiyi

- Mai magana da yawun kungiyar sojojin na Operation lafiya Dole, Onyema Nwachukwu, yace jami’an suna cikin gudanar da bincike ne a kan hanyar Konduga, inda aka yaudare su da dattijon wanda ya shige masu da zimmar su bincike shi

- Amfanin da Boko Haram suka yi da Dattijon yasa jami’an tsaron basu ankara da mike faruwa ba har ya aiwatar da abunda ya fito yi, saboda ‘yan kungiyar amfi saninsu da yin, amfani da kananan yara matasa maza da mata wurin aiwatar da ta’addancinsu

Hukumar sojojin Najeriya tace harin da aka kai a ranar Talata wanda yayi sanadiyar rayukan jami’an tsaro na kato da gora uku a Konduga dake jihar Borno, sunyi nasara ne ta hanyar amfani wani da dattijo wanda yayi shiga ta matafiyi gajiyayye.

Mai magana da yawun kungiyar sojojin na Operation lafiya Dole, Onyema Nwachukwu, yace jami’an suna cikin gudanar da bincike ne a kan hanyar Konduga, inda aka yaudare su da dattijon wanda ya shige masu da zimmar su bincike shi.

Kungiyar Boko Haram sun bulo da wani sabon salo na kai harin kunar bakin wake
Kungiyar Boko Haram sun bulo da wani sabon salo na kai harin kunar bakin wake

Amfanin da Boko Haram suka yi da Dattijon yasa jami’an tsaron basu ankara da mike faruwa ba har ya aiwatar da abunda ya fito yi, saboda ‘yan kungiyar amfi saninsu da yin, amfani da kananan yara matasa maza da mata wurin aiwatar da ta’addancinsu.

KU KARANTA KUMA: Ramadan: Buhari ya aika sakon gaisuwa ga Musulmai, ya bukaci da su nuna soyayya ga yan Adam

Sakamakon hakan dattijon ya shige masu domin su bincike shi ba tare da sun fahimci dan kungiyar Boko Haram bane, ya tayar da bam din dake ciki ledar tasa da yake dauke da ita, inda ya kashe kansa da kuma jami’an tsaro na kato da gora uku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel