Goron Watan Ramadan: Me ya hallata ga mai azumi a cikin wannan watan?

Goron Watan Ramadan: Me ya hallata ga mai azumi a cikin wannan watan?

Akwai bukatar a san abubuwan da ke karya azumi a Watan Ramadan. A baya mun kawo jerin abubuwan da ke kai Musulumi yayi kaffara bayan Azumi don haka wannan karo mun kawo wasu abubuwan da mai azumi zai iya yi kuma ba tare da azumin sa ya karye ba.

Goron Watan Ramadan: Me ya hallata ga mai azumi a cikin wannan watan?
Bayin Allah an dukufa ana ibada a cikin Watan Azumi

Manyan Malaman Musulunci sun ce sunbantar mace da kuma irin su dandana abinci ba su karya azumi. Ga dai jerin abubuwan da ba za su kai mutum ga kaffara nan ba kamar haka:

1. Amfani da turare

Komai karfin turare da kanshin sa ba ya karya azumi inji Malamai. Malaman Musulunci sun ce muddin ba a sha turaren ba babu damuwa. Kwalliya a jiki ma bai isa karya azumi ba.

2. Habo

Ko da kaho da rana tsaka bai halatta amma habo idan ya zo wa mutum bai nufin azumin sa ya karye. Sai dai Malamai sun ce a guji hadiyar jinin. Haka kuma dibar jini domin ayi gwaji bai karya azumi.

KU KARANTA: Abubuwa 5 da ke jawo mai azumi yayi kaffarar kwanaki 60

3. Runguma da sumbantar mace

Don mutum ya kai ga rungumar matar sa ko ya sumbance ta a cikin Watan Ramadan bai karya azumi muddin ba a kai makura wajen tada sha’awa ba. Fitan ruwan da maniyyi ba bai nufin azumi ya karye.

4. Dandana abinci

Haka kuma mai azumi zai iya dandana abincin da ake shiryawa na buda-baki. Abin da bai halatta ba dai shi ne a hadiye abinci. Haka kuma goge baki bai karya azumi sai an hadiyi man gogewar.

5. Mafarki

Mafarkin mace ko makamancin sa ma bai karya azumi. Mai azumin zai yi wankan janaba ne ya cigaba da azumin sa ba tare da wani ramuwa ba inji Malamai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel