Abubuwan da ke kai Musulumi yayi kaffara cikin Azumi

Abubuwan da ke kai Musulumi yayi kaffara cikin Azumi

Mun kawo maku goron Watan azumi inda mu ka jero maku abubuwan da ke karya azumi a addinin Musulunci. Manyan Malaman Musulunci na Duniya irin su Sheikh Al-Uthaymeen ne su ka bada wadannan fatawowi.

Bayan cin abinci ko shan wani abu, kaho na cikin abubuwan da ke karyawa Musulumi azumin sa Inji Malaman Musulunci.

Abubuwan da ke kai Musulumi yayi kaffara cikin Azumi
Taron Musulumi su na ibada a cikin watan Azumi

Ga dai abubuwan da ke jawo mai azumi yayi kaffara nan kamar haka:

1. Ci, sha da sauran su

Hakika a lokacin da ake azumi ba a cin abinci kuma ba a shan ruwa da gan-gan. Haka nan kuma bai yiwuwa mai azumi ya busa sugari ko wani abu makamancin sa.

2. Saduwa da mace

Da zarar mai azumi ya sadu da matar sa a cikin rana to azumin sa ya karye. Jima’i a tsakiyar rana zai haifawa mutum kaffara na kwanaki 60 a jere.

KU KARANTA: Saudi ta bayyana lokacin da za a fara azumin bana

3. Wasa da gaba

Bayan saduwa da mace kuma wasa da gaba har ta kai ga inzali ma yana karya azumi. Idan ba a kai ga inzali ba kuwa azumin na nan amma da nakasa.

4. Allurar abinci

Ba kowace allura ce ke karya azumi ba amma allurar da ake yin ta a madadin tuwo domin maras lafiya ya samu karfi a jikin sa tana karya azumi.

5. Kaho

Malaman addini sun ce bai halatta wanda yake azumi yayi kaho da rana tsaka. A kan yi kaho ne domin cire jinin da yayi sanyi ya daskare a jikin mutum.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel