Yanzu-Yanzu: A gobe Laraba za a shigar da Kasafin Kudi na 2018 - Majalisar Wakilai

Yanzu-Yanzu: A gobe Laraba za a shigar da Kasafin Kudi na 2018 - Majalisar Wakilai

A yayin zaman majalisar wakilai da aka gudanar a ranar yau ta talata, majalisar ta bayyana cewa a gobe Laraba ne a za a shigar da sabon kasafin kudin 2018 cikin doka.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Jaridar The Punch ta ruwaito, za a shigar da kasafin kudin cikin doka na kimanin N9.12trn sabanin yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar na N8.61trn tun kimanin watanni shidda da suka gabata.

Wanda ya jagoranci zaman majalisa na yau mataimakin kakakin majalisar, Yussuff Lasun, shine ya bayyana hakan yayin karbar sakamakon binciken kwamitin kasafin kudi wanda Mustapha Dawaki ya jagoranta.

Wannan sabon kasafin kudi na N9.12trn da ya sha kwaskwarima ya samu doriya ta N410bn akan N8.61trn da shugaba Buhari ya gabatar tun a watan Nuwamba na 2017 da ya gabata.

Yanzu-Yanzu: A gobe Laraba za a shigar da Kasafin Kudi na 2018 - Majalisar Wakilai

Yanzu-Yanzu: A gobe Laraba za a shigar da Kasafin Kudi na 2018 - Majalisar Wakilai

Lasun ya nemi dukkanin wakilai na majalisar a kan samun takardu na shaidar kasafin kudin da kwamitin ya gabata sakamakon yiyuwar sanya shi cikin doka a gobe Laraba.

KARANTA KUMA: Dakarun Soji sun ceto wani Dattijo daga hannun 'yan Ta'addan Boko Haram a jihar Borno

NAIJ.com ta fahimci cewa, an samu nukusani na shigar da kasafin kudin cikin doka sakamakon wasu ma'aikatu da cibiyoyin gwamnati da suka kawo tangarda kamar yadda majalisar zantarwa ta kasa ta kalubalanta.

A sanadiyar wannan tsaiko ne ya sanya shugaba Buhari bayar da umarni ta doka mai kayyade lokacin fitar da kididdigar kasafin kudi ga ma'aikatu da cibiyoyin gwamnatin tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kwankwaso ya tsayar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Da duminsa: Kwankwaso ya fitar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Kwankwaso ya tsayar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP
NAIJ.com
Mailfire view pixel