Shugaba Buhari ya bayyana rawar da gwamnatin sa ta taka cikin shekaru 3

Shugaba Buhari ya bayyana rawar da gwamnatin sa ta taka cikin shekaru 3

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin sa ta taki nasara wajen cimma manufofin da ta sanya a gaba ta hanyar tattalin kankanin arzikin kasa da ya taras gami da kawo tsare-tsare da suka dakile almubazzaranci a kasar nan.

Babban kakakin shugaban kasa na musamman, Mallam Garba Shehu, shine ya bayyana hakan da sanadin wata sanarwa da shugaba Buhari yayin ziyarar jihar Jigawa a ranar Litinin din da ta gabata.

Kafar watsa labarai ta Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya yi wannan furuci ne a fadar mai marataba Sarkin Dutse, Alhaji Buhu Muhammadu Sanusi dake garin na Dutse a jihar Jigawa.

Shugaba Buhari ya bayyana rawar da gwamnatin sa ta taka cikin shekaru 3

Shugaba Buhari ya bayyana rawar da gwamnatin sa ta taka cikin shekaru 3

Shugaba Buhari yake cewa duk da badakalar ta farashin man fetur a kasuwanni duniya, hakan bai kawo karayar gwiwa ta gwamnatin sa na wajen cimma manufofin ta na kawo ci gaba a kasar nan.

KARANTA KUMA: Hukumomin Hisbah da FRSC sun tanadi Ma'aikata 830 domin ziyarar Buhari jihar Jigawa

NAIJ.com da sanadin rahoton na jaridar Daily Trust ta fahimci cewa, kwazon da gwamnatin shugaba Buhari ta yyi cikin shekaru uku ya yiwa wanda jam'iyyar PDP ta aiwatar cikin shekaru 16 na mulkin kama karya da ta yiwa kasar nan.

A nasa jawabin, sarkin Dutse ya yabawa gwamnatin tarayya dangane da kwazon ta na tunkara matsaloli rashawa, ta'addanci da kuma ta'ammali da fataucin muggan kwayoyi da ke kawo zagon kasa a cikin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka

Zai yi wuya Buhari ya lashe zaben 2019 - Cibiyar bincike a Amurka

Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka
NAIJ.com
Mailfire view pixel