Aiki ga mai kareka: Buratai ya bawa Sojoji wa’adin makwanni 3 su gama da ‘yan tada kayar baya a Birnin Gwari

Aiki ga mai kareka: Buratai ya bawa Sojoji wa’adin makwanni 3 su gama da ‘yan tada kayar baya a Birnin Gwari

- Sojojin Najeriya sun yi babban hubbasa a yunkurin tabbatar da tsaro a kasar nan

- Sakamako yawaitar hare-haren 'yan Bindiga a yankin Birnin Gwari dake jihar Kaduna, rundunar Sojojin tayi azamar girke Bataliya guda don maganin masu kashe Mutane da kona kadarorinsu

Shugaban rundunar Sojin Najeriya Tukur Buratai ya kaddamar da Atisayen ‘Idon Raini’ a karkashin shirye-shiryen jibge bataliyar Sojoji a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Aiki ga mai kareka: Buratai ya bawa Sojoji wa’adin makwanni 3 su ga bayan ‘yan tada kayar baya a Birnin Gwari
Aiki ga mai kareka: Buratai ya bawa Sojoji wa’adin makwanni 3 su ga bayan ‘yan tada kayar baya a Birnin Gwari

Tukur Buratai ya ce ya zama dole ga Sojojin da su tabbata sun taka rawar gani ta hanyan kawo karshen aiyukan ‘yan Bindiga da suka addabi yankin cikin makwanni uku.

“Ba zamu cigaba da jiran sai an kawo muku hari sannan ku kare kanku ba, tilas ku bisu har maboyarsu ku tabbata kun ga bayansu domin su ne suka fara takalarku. Dole ne wannan kashe-kashen da lalata dukiyar jama’a a dakatar da shi, ba ma iya Kaduna ba hatta sauran jahohin kasar nan baki daya.”

KU KARANTA: Zamu rarrabawa ‘yan Najeriya kudaden da Abacha ya sata – Shugaba Buhari

Buratai ya cigaba da cewa, “Nan da makwanni biyu zuwa uku dole ne mu gani a kasa, tun da dai tsagerun ba daga Duniyar wata suke fitowa ba, lallai kuna binsu har maboyarsu kuna gamawa da su.”

Aiki ga mai kareka: Buratai ya bawa Sojoji wa’adin makwanni 3 su ga bayan ‘yan tada kayar baya a Birnin Gwari
Aiki ga mai kareka: Buratai ya bawa Sojoji wa’adin makwanni 3 su ga bayan ‘yan tada kayar baya a Birnin Gwari

Da yake karbar bakuncin shugaban Sojojin a fadarsa Mai Martaba Sarkin Birnin Gwari Zubairu Jibril Mai Gwari II, ya bayyana kwarin gwuiwarsa ga rundunar inda ya ce da taimakon Sojojin da za’a jibe a yankin har bataliya guda, yana da yakinin za’a iya fatattakar ‘yan Bindigar cikin kankanin lokaci.

Kana yayi roko ga babban Hafsan Sojojin da ya sake turo da dakarun da aka dauke daga yankin domin suyi taka rawar gani.

Daga karshe Buratai ya tabbatarwa da Sojojin biya musu duk bukatunsu na jin dadi da walwalarsu domin su ji dadin gudanar da aikinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel