Da dumin sa: An saki sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Kaduna, karanta yadda ta kaya

Da dumin sa: An saki sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Kaduna, karanta yadda ta kaya

Jam’iyyar adawa ta PDP tayi nasarar lashe kujerar shugaban karamar hukumar Zangon Kataf da kansilolin yankin gaba daya, kamar yadda kamfanin dillancinlabarai (NAN) ya rawaito.

Baturen zabe a karamar hukumar, Danjuma Baye-Luka, ya sanar da sakamakon da safiyar yau, Lahadi, a Zonkwa.

Ya bayyana cewar, dan takarar jam’iyyar PDP, Elias Maza, ya samu kuri’u 55,643 tare da samun nasara a kan dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, John Hassan, ya samu kuri’u 31,514.

Jam’iyyar APC ta lashe zabukan a kanan hukumomin Soba, Zaria, Lere, Ikara, Makarfi, Birnin Gwari, Giwa, Kagarko, Kudan, Igabi da Kajuru. Ana sauraron sakamako daga wasu kananan hukumomin.

Da dumin sa: An saki sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Kaduna, karanta yadda ta kaya
Gwamnan jihar Kaduna; Nasir El-Rufa'i
Asali: UGC

Kudan ce karamar hukumar da Sanata, Suleiman Hunkuyi, da basa-ga-maciji da gwaman jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’I ya fito.

Kazalika jam’iyyar APC tayi nasara a karamar hukumar Makarfi ta tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi.

DUBA WANNAN: Tinubu ya gano mutanen da suka haddasa rikici yayin zabukan jam'iyyar APC

Dan takarar El-Rufai ya yi nasara a mazabar Sanata Shehu Sani Sani dake karkashin karamar hukumar Kajuru.

A karamar hukumar Zaria, APC ta samu kuri’u 42,859 yayin da PDP ta samu 16,033. A soba APC ta samu 40,903, PDP ta samu 13,835.

Jihar Kaduna ta gudanar da zabukan ne ta hanyar amfani da na’urori masu kwakwalwa a karo na farko a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel