Yunwa, rashin Tsaro da Talauci duk gwamnatin Buhari ce ta kawo su - Sule Lamiɗo

Yunwa, rashin Tsaro da Talauci duk gwamnatin Buhari ce ta kawo su - Sule Lamiɗo

- Tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari kan rashin iya gudanar da mulki, kana kuma yayi masa albishir da cewa PDP ce zata lashe zaben 2019

- Lamido ya bayyana hakan ne yayin taron karramawa da aka gudanar ga wani jigo a jam'iyyar tasu

Ɗan takarar shugabancin ƙasar nan ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP Alhaji Sule Lamiɗo, ya bayyana cewa halin matsi da yunwa da kuma matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar nan duk jam'iyyar APC ce ƙarƙashin jagorancin shugaban Muhammadu Buhari ta kawo su.

Yunwa, rashin Tsaro da Talauci duk gwamnatin Buhari ce ta kawo su - Sule Lamiɗo
Yunwa, rashin Tsaro da Talauci duk gwamnatin Buhari ce ta kawo su - Sule Lamiɗo

Sule Lamiɗo ya bayyana hakan ne a yayin taron da aka shirya na girmamawa ga mataimakin shugaban jam'iyyar PDP ta ƙasa Senator Babayo Gamawa, ranar Asabar a garin Bauchi. Lamiɗo dai yayi iƙirarin cewa a shekara ta 2015, shugaba Muhammadu Buhari tsautsayi ya sanya ya samu shugabancin ƙasar nan ba tare da ya shiryawa mulkin Najeriya ba.

KU KARANTA: Rubdugu: PDP, sabuwar jam’iyyar Obasanjo da wasu jam’iyyu 38 na yiwa Buhari wani yakin sunkuru

"Najeriya ba ƙasar Fulani ba ce su kaɗai, Musulmai da Kirista kowa yana da iko cikinta. Kuma taɓarɓarewar sha'anin tsaro a ƙasar nan babbar alama ce da ke nuna gazawar Buhari da kuma hannun da suke da shi a cikin abubuwan da suke faruwa na kashe-kashe."

Sule Lamiɗo ya ja hankalin shugaban ƙasa da ya daina amfani da sunan yaƙi da cin hanci da rashawa wajen tsorata ƴan hamayya da gwamnatinsa, domin hakan na nuni da cewa ya firgita don tunanin faɗuwa zaɓen 2019.

Lamiɗo ya kuma bayyana cikin kwarin gwuiwa cewa, a zaɓe mai zuwa su za'a rantsar domin zaɓen cikin gida da APC ta gudanar wata alama ce da ke nuni da karshenta ya zo. Kana kuma yayi kira ga ƴan Najeriya da su tabbata sun kaɗawa PDP ƙuri'unsu don korar APC daga Mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel