Shugaba Buhari ya yi alkawarin daidaita tsarin Jami'o'in Najeriya

Shugaba Buhari ya yi alkawarin daidaita tsarin Jami'o'in Najeriya

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin magance matsalolin kungiyar ASUU wajen tabbatar da daidaiton tsare-tsaren jami'o'i a fadin kasar nan.

Shugaban kasar wanda Dakta Gidado Bello Kumo na hukumar jami'o'i ta NUC ya wakilta, ya yi wannan alkawari ne a yayin bikin yaye dalibai na jami'ar Abubakar Tafawa Balewa dake jihar Bauchi a ranar Asabar din da ta gabata.

Dakta Kumo ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta dukufa wajen shawo kan matsalolin kungiyar ASUU da za ta kawo karshen afkuwa yajin aiki na jami'o'i a fadin kasar nan.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin daidaita tsarin Jami'o'in Najeriya

Shugaba Buhari ya yi alkawarin daidaita tsarin Jami'o'in Najeriya

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta kudiri aniyyar kawo sabbin tsare-tsare da za su magance wannan matsalolin gami da kalubalan karni na 21 da jami'o'in kasar nan ke fuskanta.

KARANTA KUMA: Babban Sakataren Kungiyar CAN ya riga mu Gidan gaskiya

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Dakta Kumo ya kuma kirayi dukkanin masu ruwa da tsaki wajen goyon bayan gwamnatin tarayya domin tabbatar da inganta tsare-tsaren jami'o'in kasar nan.

A nasa jawabin shugaban jami'ar Farfesa Saminu Abdulrahman Ibrahim, ya yabawa shugaba Buhari dangane da amsa goron gayyata na wannan biki tare da karfafa masa gwiwa wajen inganta sashen ilimi na jami'o'in kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka

Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka

Buhari zai iya faduwa zaben 2019, alamu sun nuna - Cibiyar binciken Amurka
NAIJ.com
Mailfire view pixel