Shekaru 5 uwargidata ta hana ni saduwa da ita, amma tana rabawa mambobin coci kyauta – Fasto

Shekaru 5 uwargidata ta hana ni saduwa da ita, amma tana rabawa mambobin coci kyauta – Fasto

Wata matar fasto mai suna, Mrs Uzoamaka Ibeneme, a yau Juma’a ta rasa aurenta a wani kotun majistare da ke zaune a jihar legas sanadiyar zinace-zinace.

Shugaban kotun, Mr Akin Akinniyi, wanda ya yanke hukucin, ya ce mijinta Fasto Joshua Ibeneme ya lashi takobin rabuwarsu duk da hakuran da dangi suka bashi.

Faston yace: “Uwargidata tana zinace-zinace da mambobin cocina. Kuma mambobin suna fadawa sauran yan cocin cewa sun kwanta da ita ne saboda ta neme su.

“Duk lokacin da na dawo daga tafiya, yaro na yakan fada min wasu mazaje suna daukan uwargidata. Ko ubangiji ya fada min in sake ta.”

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai dawo Najeriya yau

“Shekara biyar tana hana ni kwanciya da ita; duk lokacin da na nemi saduwa sai ta fara bani wasu uzurori, a yanzu ma haka ta raba daki da ni. Amma tana rabawa mambobin coci kyauta."

Alkalin kotun ya duk da kokarinda jama'a da dangi sukayi domin sulhuntasu, faston ya ki yarda saboda haka ya zama wajibi kotu ta raba auren.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Kwankwaso ya tsayar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Da duminsa: Kwankwaso ya fitar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP

Kwankwaso ya tsayar da dan takararsa na gwamnan Kano da mataimaki a PDP
NAIJ.com
Mailfire view pixel