Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai dawo Najeriya yau

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai dawo Najeriya yau

Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari zai baro kasar Birtaniya da yammacin yau Juma;a, 11 ga watan Mayu, 2018 bayan ya je ganawa da likitansa.

NAIJ.com ta samo wannan rahoto ne daga jam'iyyar APC reshen kasar Ingila yayinda suka kai masa shugaba Buhari ziyara a gidan gwamnati dake Ingila.

Jawabinsu yace: "Mun kaiwa shugaba Buhari ziyara gabanin dawowarshi Najeriya da ranan nan"

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai dawo Najeriya yau

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai dawo Najeriya yau

NAIJ.com ta kawo muku rahoton cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyanawa daukacin al’umman Najeriya cewa zai garzaya kasar Birtaniya gobe Talata, 8 ga watan Mayu domin ganin likitansa amma zai dawo ranan Asabar 12 ga watan Mayu idan Allah ya yarda.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne da daren nan misalin karfe 9 na dare ta shafin sada ra’ayi da zumuntarsa na Facebook dinsa.

Yace: “ Zan tafi kasar Birtaniya gobe domin ganin likita. Zai yi kwanaki 4 kuma ya dawo ranan Asabar, 12 ga watan Mayu. Fadar shugaban kasa ta saki jawabi akan haka. Zan je jihar Jigawa ranan Litinin da Talata makon gobe idan na dawo.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta NAIJ.com Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tattalin arziki: Najeriya na iya sullubawa ta koma cikin qaqa-nika yi - CBN tayi kashedi

Tattalin arziki: Najeriya na iya sullubawa ta koma cikin qaqa-nika yi - CBN tayi kashedi

Tattalin arziki: Najeriya na iya sullubawa ta koma cikin qaqa-nika yi - CBN yayi kashedi
NAIJ.com
Mailfire view pixel