Gawurtacciyar mai safarar miyagun kwayoyi ta yi batan dabo a Arewa

Gawurtacciyar mai safarar miyagun kwayoyi ta yi batan dabo a Arewa

Wata gawurtacciyar Hajiya mai safarar miyagun kwayoyi mai suna Hajiya Abu Musa wadda aka fi sani da Mata Masu shaye-shaye yanzu haka tayi batan dabo a jihar Kebbi bayan ta sulalewa jami'an hukuma.

Shugaban hukumar nan dai ta gwamnatin tarayya dake hana sha da shafarar miyagun kwayoyi watau (NDLEA) turance na jihar Kebbi dake yankin Arewa ta yamma mai suna Alhaji Suleiman Jadi shine ya sanar da hakan.

Gawurtacciyar mai safarar miyagun kwayoyi ta yi batan dabo a Arewa
Gawurtacciyar mai safarar miyagun kwayoyi ta yi batan dabo a Arewa

KU KARANTA: Ana rigimar kan iyaka a tsakanin jahohin arewa 2

Legit.ng ta samu cewa Hajiya Abu Musa wadda yar asalin karamar hukumar Kojko-Bese ce an kiyasata cewa ta shafe kimanin shekaru 20 tana wannan mugunyar sana'ar.

A wani labarin kuma, Wata kotun majistare dake zaman ta a garin Ifo dake a jihar Ogun a ranar Alhamis din da ta gabata ta bayar da umurnin cigaba da tsare wani babban malamin addinin kirista kuma shugaban majami'un Holy Garden Ministry mai suna Tobiloba Ipense.

Kamar dai yadda muka samu, kotun dai tana sauraron karar da aka shigar mata inda ake zargin babban malamin da kashe wata masoyiyar sa mai suna Raliat Sanni tare da binne ta a wani boyayyen wuri.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel