Karin matsayi: Za a nada Dambazau Baraden Kano

Karin matsayi: Za a nada Dambazau Baraden Kano

Masarautar Kano na shirin nadawa ministan harkokin cikin gida, Janar Abdulrahman Dambazau sarauta.

A ranar 11 ga watan Mayu ne za’a nada shi a matsayin Baraden Kano.

Sarkin Kano ne Muhammadu Sanusi II zai nada shi a fadar sa.

Karin matsayi: Za a nada Dambazau Baraden Kano
Karin matsayi: Za a nada Dambazau Baraden Kano

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, za ayi bukin nadin ne a fadar sarkin Kano in da ake shirin amsar bakuntar manyan baki daga kasar nan har daga kasashen waje.

KU KARANTA KUMA: 2019: Obasanjo ya zabi Jam’iyyar da zai shiga

A halin dan ake ciki Legit.ng ta kawo cewa gawar marigayi Sheikh Isiyaka Rabi’u ya iso gida Najeriya daga birnin Landan.

Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci dauko gawar a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano a safiyar yau Juma’a, 11 ga watan Mayu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel