Shugaban kasar Amurka da na Koriya ta Arewa za su yi ganawar keke-da-keke

Shugaban kasar Amurka da na Koriya ta Arewa za su yi ganawar keke-da-keke

Da alama dai duniya na gaf da shaida muhimmiyar rana mai cike da dumbin tarihi biyo bayan saka ranar tattaunawa da shugabannin kasashen Amurka Donald Trump da kuma Koriya ta Arewa Kim Jong Un da a da basu ga maciji da juna.

Kamar dai yadda muka samu, shugabannin biyu yanzu haka sun saka ranar 12 ga watan Yuni mai kamawa a matsayin ranar da za su yi ganawar tare kuma da saka kasar Singapore a matsayin wurin taron.

NAIJ.com ta samu cewa a baya dai shugabannin biyu sun yi ta nunawa juna yatsa tare da jifar juna da kalaman takalar fada tsakanin su.

A wani labarin kuma, Mataimakan gwamnonin jahohin Zamfara da kuma Sokoto dukan su da ke a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya kuma masu makwaftaka da juna sun jagoranci gudanar da wani muhimmin taro da nufin warware takaddamar kan iyakar su.

Taron dai wanda ya gudana a garin Sokoto ya samu halartar jami'an gwamnatocin jahohin da ma kuma hukumar kula da kan iyakoki ta gwamnatin tarayya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain NAIJ.com HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-yanzu: Janar AbdulSalam Abubakar, shugaban INEC sun shiga ganawar sirri kan zaben jihar Osun

Yanzu-yanzu: Janar AbdulSalam Abubakar, shugaban INEC sun shiga ganawar sirri kan zaben jihar Osun

Yanzu-yanzu: Janar AbdulSalam Abubakar, shugaban INEC sun shiga ganawar sirri kan zaben jihar Osun
NAIJ.com
Mailfire view pixel